Bayan Faduwa Zaɓen Anambra, Yar Takarar Gwamna Ta Gayyaci Mutanen da Suka Kada Mata Kuri'a
- Fitacciyar jaruma kuma ƴar takarar gwamna a zaɓen Anambra da ya gabata, Chioma Ifemeludike ta faɗi zaɓe
- Sai dai ba ta bar lamarin ya cuzguna mata ba, inda ta gayyaci mutanen da suka kaɗa mata kuri'a zuwa liyafar cin abinci
- Jarumar, wacce ta tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar AAC, ta samu ƙuri’u 292 rumfunan zaɓe 5,718 a ƙananan hukumomin jihar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Anambra – Fitacciyar jarumar fina-finai ta Nollywood, Chioma Ifemeludike, wadda aka fi sani da IfeDike, ta nuna farin ciki ga mutanen da suka kaɗa mata ƙuri’a a zaɓen gwamnan Jihar Anambra.
Ifemeludike ta tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar AAC inda ta samu ƙuri’u 292 kacal daga rumfunan zaɓe 5,718 da aka samar a ƙananan hukumomin da ke fadin jihar.

Kara karanta wannan
Zaben Anambra: Dan takarar jam'iyyar Labour ya barranta da sakamakon zaben gwamna

Source: Facebook
Sai dai maimakon ta nuna bacin rai ko takaicin faduwa zabe, jarumar ta zabi ta yi ta zauna da mutanen da suka kada mata kuri'a, inda ta aika masu goron gayyata ta shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yar takarar gwamnan Anambra ta gayyaci masoyanta
A wani saƙon da ta wallafa, Chioma ta nuna farin cikinta a kan yadda mutanen da ba su kai 300 ba suka zabe ta, tare da gayyatar liyafar cin abinci.
Sakon ya ce:
“’Mutane 292 da suka kada min kuri'a, yaushe za mu yi liyafar cin abinci, mu sha giya mu rungume juna? Ina ɗokin wannan zama. Na gode, ina ƙaunarku."
Ifemeludike ta nemi a zabe ta bisa manufar haɗin kai da ci gaban jama’a, inda ta yi alkawarin samar da makamashi mai amfani da hasken rana.

Source: Original
A lokacin da ta ke yawon neman kuri'a a jihar, ta yi alkawarin samar da rangwame a kudin makaranta, da kuma ƙara tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar. Amma a zaɓen da aka yi, Gwamna Charles Soludo na jam’iyyar APGA, wanda ya samu ƙuri’u 422,664.
Yadda yar takarar gwamnan Anambra ta yi kamfen
A yayin kamfen, jarumar ta yi alfahari da gogewarta a matsayin ’yar ƙungiyar ma’aikata da kuma tsohuwar shugabar jam’iyyar AAC a jihar, wanda ta ce ya taimaka mata wajen fahimtar bukatun talakawa.
Baya va harkokin siyasa kuma, Ifemeludike ta dade tana taka rawa a fagen shirya fina-finai a Nollywood.
Ta fara shahara ne da jerin shirinta na YouTube mai suna Corpers Heaven, wanda ya samo asali daga ƙwarewarta a lokacin aikin NYSC.
Tun daga lokacin, ta ci gaba da fice da fina-finai irin su ‘Painful Truth’, ‘Commissioner for Happiness’, ‘Mortuary Gate’, ‘Plantain Girl’ da ‘Made in Heaven’, waɗanda suka taimaka wajen gina sunanta a masana’antar Nollywood.
Dan takarar gwamnan Anambra ya fusata
A baya, mun wallafa cewa dan takarar APC, Nicholas Ukachukwu, ya bayyana matsayarsa game da nasarar Charles Soludo na jam’iyyae APGA a zaɓen Anambra.
Ukachukwu ya bayyana cewa jam’iyyar APC tana tattara bayanai daga mazabu zuwa kananan hukumomi kafin yanke hukunci a kan yiwuwar tafiya kotu kan zaɓen.
Ukachukwu ya gode wa magoya bayansa da yan jam’iyyar APC bisa jajircewar su a lokacin kamfen da lokacin zaɓen, inda ya koka a kan yadda ya ce an tsangwame su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

