Shugaba Tinubu Ya Yi Magana kan Zaben Anambra, Ya Aika Sako ga Gwamna Soludo

Shugaba Tinubu Ya Yi Magana kan Zaben Anambra, Ya Aika Sako ga Gwamna Soludo

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tsokaci kan zaben gwamnan jihar Anambra da aka gudanar a ranar Asabar
  • Mai girma Bola Tinubu ya taya Gwamna Charles Chukwuma Soludo kan nasarar da ya samu a zaben
  • Shugaban kasan ya kuma yi tsokaci kan rawar da hukumar zabe ta INEC ta taka wajen gudanar da sahihin zabe a jihar Anambra

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Charles Soludo, murnar sake lashe zaben gwamna.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa nasarar ta tabbatar da cewa tsare-tsaren gwamnatinsa suna haifar da sakamako mai kyau ga al’umma.

Tinubu ya taya Soludo murnar lashe zabe
Shugaba Bola Tinubu tare da Gwamna Chukwuma Soludo Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa a ranar Lahadi, wadda Bayo Onanuga ya sanya a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Gwamna Soludo ya aika sako ga Tinubu bayan lallasa dan takarar APC a zaben Anambra

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Tinubu ya ce kan nasarar Gwamna Soludo?

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa sakamakon zaben ya nuna amincewar jama’a kan hangen nesa da shugabancin Soludo.

“Nasara mai rinjaye da ya samu a zaben ranar Asabar ta tabbatar da cewa Farfesa Soludo ya zama na uku a tarihin Anambra da ya samu wa’adi na biyu."
'Wannan alama ce ta jagoranci mai hangen nesa da kuma ci gaban da jihar ta samu karkashinsa.”

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaban kasa ya yaba da yadda Soludo ya mayar da iliminsa da kwarewarsa kan harkokin tattalin arziki zuwa aiki na zahiri a gwamnati, yana mai cewa hakan ya nuna yadda ilimi ke iya samar da ci gaba mai dorewa.

Tinubu ya yabawa shugaban INEC

Tinubu ya kuma yaba wa mutanen Anambra, jami’an tsaro, da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) saboda yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da gaskiya, yana mai cewa hakan hujja ce ta karuwar wayewar dimokuradiyya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Abin da Soludo ya ce bayan samun wa'adi na 2

Ya jinjinawa sabon shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, da tawagarsa saboda gudanar da abin da ya kira zabe nagari kuma sahihi, yana mai bukatar hukumar ta ci gaba da dorawa kan wannan kwarewar.

Wace shawara Tinubu ya ba Soludo?

Tinubu ya bukaci Soludo da ya nuna karimci da haɗin kai bayan nasara, yana mai cewa ya kamata ya nemi hadin kai daga abokan hamayyarsa domin ci gaba da gina Anambra mai hadin kai da arziki.

Shugaba Tinubu ya taya Soludo murna
Mai girma Bola Tinubu tare da Gwamna Chukwuma Soludo Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter
"Ina tabbatar wa Gwamna Soludo da cikakken goyon bayana, kuma ina fatan ci gaba da hadin kai tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihar Anambra.”

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya ce sake nasarar Soludo karkashin jam’iyyar APGA ta nuna karfin dimokuradiyyar Najeriya, inda aiki da cancanta ke fice fiye da bambancin jam’iyyu.

"Nasarar jam’iyyar adawa ta APGA ta nuna cewa shugaba mai aiki tukuru da hangen nesa ba za a iya hana shi nasara ba.”

- Shugaba Bola Tinubu

Soludo ya yabawa Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Anambra ya aika sako ga Mai girma Bola Tinubu bayan sake lashe zabe.

Kara karanta wannan

Anambra: An fadi yawan ƙananan hukumomi da Soludo ya lashe, ya nakasa APC

Gwamna Soludo ya yabawa shugaban kasan kan tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.

Hakazalika, ya yabawa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, kan gudanar da sahihin zabe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng