Gwamna Soludo Ya Aika Sako ga Tinubu bayan Lallasa dan Takarar APC a Zaben Anambra
- Mutanen jihar Anambra sun sake zaben Gwamna Charles Chukwuma Soludo a matsayin wanda zai ci gaba da mulkarsu har na tsawon shekara hudu
- Gwamna Soludo ya nuna matukar godiyarsa ga mutanen jihar kan amanar da suka sake damkawa a hannunsa
- Hakazalika, Gwamna Soludo ya aika da sako ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayn nasarar da ya samu a zaben
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Anambra - Gwamna Chukwuma Soludo ya kwararo yabo ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan zaben gwamnan jihar Anambra.
Gwamna Soludo ya gode wa Shugaba Tinubu bisa jajircewarsa wajen tabbatar da sahihin tsarin zaɓe a Anambra.

Source: UGC
Jaridar Vanguard ta ce Gwamna Soludo ya yi wannan godiya ne a ranar Lahadi, 9 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Soludo ya yi godiya ga Tinubu
Ya yi godiyar ne yayin jawabin nasara bayan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna na ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamba, 2025.
Gwamna Soludo ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa tsayuwarsa a kan ka’idojin dimokuraɗiyya, yana mai cewa shugaban kasan ya tabbatar da cewa zaɓen ya gudana cikin gaskiya da adalci.
“Da cikakkiyar godiya ga shugaban kasa kuma babban kwamandan sojoji, ina gode wa Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu bisa kasancewarsa cikakken ɗan dimokuraɗiyya."
"Ya nuna jajircewa wajen tabbatar da sahihin zaɓe mai cike da adalci”
- Gwamna Chukwuma Soludo
Soludo ya yabawa shugaban INEC
Gwamnan ya kuma yaba wa shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, yana mai bayyana zaɓen a matsayin mafi inganci da aka gudanar a jihar tun bayan fara amfani da fasaha cikin tsarin zaɓe.
“Wannan shi ne gwajin ka na farko, kuma abin farin ciki ne cewa wannan gwaji naka na farko ya bar kyakkyawan tarihi. INEC ta yi abin kirki."
- Gwamna Chukwuma Soludo
Soludo, wanda ya samu wa’adi na biyu tare da mataimakinsa Onyeka Ibezim, ya ce sakamakon ya nuna a fili irin amincewar jama’a da gwamnatinsa.
Soludo ya godewa mutanen Anambra
Ya lura cewa wannan zaɓen ya samu ɗaya daga cikin mafi yawan halartar masu kada kuri’a a tarihin siyasar jihar.

Source: Twitter
“Na fito ne kawai na gode muku da ‘Ndi Anambra’. Wannan lokaci ne na taya juna murna. Kun yi magana."
“Shekaru huɗu da suka wuce, kun zaɓe mu da kimanin kuri’u 112,000. A wannan karon, kun yi magana da ƙarfi. Wannan nasara ba kawai nasara ba ce, tarihi ne da kuka kafa.”
- Gwamna Chukwuma Soludo
Ya bayyana cewa kusan kashi 22 cikin 100 na masu rajista sun fito suka kada kuri’a, abin da ya kira abin da bai taɓa faruwa ba a baya.
Soludo ya yi magana kan nasararsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo, ya yi magana kan nasarar da ya samu.
Gwamna Soludo ya yabawa mutanen jihar kan sake zabensa da suka yi a karo na biyu domin ci gaba da jagorantarsu.
Hakazalika ya yi musu alkawarin cewa za su ga gagarumin ci gaba a cikin shekara hudu masu zuwa nan gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

