Sakamakon Zaben Anambra: Yadda APGA Ta Samu Kuri'u 422,664 a Kananan Hukumomi 21

Sakamakon Zaben Anambra: Yadda APGA Ta Samu Kuri'u 422,664 a Kananan Hukumomi 21

  • Gwamna Charles Soludo na jam’iyyar APGA ya lashe dukkanin kananan hukumomi 21 a zaben gwamnan jihar Anambra
  • Hukumar INEC ta sanar da cewa APGA ta samu kuri’u 422,664, yayin da APC ta samu 99,445, LP 10,505, sannan PDP 1,401
  • INEC ta ce za ta bayyana sakamakon karshe bayan kammala ƙididdigar da jami’an zabe ke yi a Awka, babban birnin jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kammala tattara sakamako daga rumfunan zabe 5,718 da ke cikin kananan hukumomi 21 na Anambra.

Wannan na zuwa ne bayan da aka kammala zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar, 8 ga Nuwamba, 2025.

Gwamna Charles Soludo ya samu nasarar lashe zaben Anambra
Gwamna Charles Soludo a taron rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a zaben Anambra. Hoto: @CCSoludo
Source: Twitter

Tattara sakamakon ya fara ne da misalin ƙarfe 12:00 na dare zuwa ƙarfe 8:00 na safiyar Lahadi, karkashin jagorancin Farfesa Edogah Omoregie, shugaban jami’ar Benin, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Bidiyo: An ga 'yan sanda suna harba bindiga bayan Soludo ya lashe zaben Anambra

Wannan aikin tattara sakamakon ya gudana ne tare da sa ido daga jami’an INEC, wakilan jam’iyyun siyasa, da manema labarai.

INEC: 'Soludo ya lashe zaben Anambra'

Daga sakamakon da aka bayyana, dan takarar APGA, Farfesa Charles Chukwuma Soludo, ya yi nasara a dukkan kananan hukumomi 21, a tazarar kuri'u masu yawa.

A cewar Farfesa Charles Chukwuma, 'yan takara 16 daga jam'iyyu daban daban ne suka shiga zaben gwamnan jihar na Anambra.

Ya bayyana cewa, an tantance masu kada kuri'a 598,229 daga cikin 2,788,864 da aka yi wa rajista, kuma 595,298 sun yi zabe yayin da aka ki karbar kuri'u 11,244 a fadin kananan hukumomi 21.

"Bayan kammala tattara sakamakon zaben kamar yadda yake kunshe a fom mai lamba EC8E, yanzu zan iya sanar da kuri'un da kowane dan takara ya samu da jam'iyyarsa.
"Ni Farfesa Edoba Omoregie, jami'in tattara sakamakon zaben gwamnan Anambra na 2025, na ayyana cewa zaben ya gudana cikin lumana. Kuma, Chukwuma Soludo na jam'iyyar APGA ya samu kuri'u 422,664.

Kara karanta wannan

Anambra: Bayan kai ruwa rana, INEC ta sanar da wanda ya lashe zaben gwamna

"Saboda shi ne ya samu kuri'u mafi rinjaye da aka kada a zaben, na ayyana shi a matsayin wanda ya lashe wannan zabe, bayan cika dukkan sharudan doka."

Yayin da Soludo da jam'iyyarsa ta APGA suka samu kuri'u 442,664 a zaben, jaridar The NAtion ta rahoto cewa sauran jam'iyyu sun samu kuri'u kamar haka:

INEC ta sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra
Hoton cibiyar tattara sakamakon zaben gwamnan Anambra da ke a hedikwatar INEC, a birnin Awka. Hoto: @SituationRoomNg
Source: Twitter

Anambra: sakamakon zabe a kananan hukumomi 21

Dunukofia: ADC – 232 | APC – 3,284 | APGA – 14,892 | PDP – 16

Njikoka: ADC – 236 | APC – 5,687 | APGA – 22,213 | PDP – 47

Awka North: ADC – 815 | APC – 3,661 | APGA – 15,895 | PDP – 203

Aguata: ADC – 301 | APC – 4,125 | APGA – 35,559 | PDP – 82

Orumba ta Kudu: ADC – 361 | APC – 2,828 | APGA – 19,818 | PDP – 18

Orumba ta Arewa: ADC – 115 | APC – 2,615 | APGA – 24,664 | PDP – 17

Kara karanta wannan

Anambra 2025: Soludo ya lallasa APC, LP, ya ci zabe a dukkan kananan hukumomi 21

Oyi: ADC – 167 | APC – 5,118 | APGA – 18,882 | PDP – 16

Anambra ta Gabas: ADC – 157 | APC – 3,108 | APGA – 14,665 | PDP – 207

Ayamelum: ADC – 470 | APC – 7,478 | APGA – 13,340 | PDP – 13

Nnewi ta Arewa: ADC – 553 | APC – 5,441 | APGA – 20,320 | PDP – 45

Nnewi ta Kudu: ADC – 127 | APC – 9,281 | APGA – 17,286 | PDP – 12

Ogbaru: ADC – 465 | APC – 3,768 | APGA – 22,803 | PDP – 30

Onitsha ta Arewa: ADC – 514 | APC – 4,677 | APGA – 24,225 | PDP – 111

Onitsha ta Kudu: ADC – 231 | APC – 4,156 | APGA – 15,742 | PDP – 73

Anaocha: ADC – 255 | APC – 5,956 | APGA – 20,118 | PDP – 42

Idemili ta Arewa: ADC – 722 | APC – 6,383 | APGA – 25,498 | PDP – 125

Kara karanta wannan

Anambra: An fadi yawan ƙananan hukumomi da Soludo ya lashe, ya nakasa APC

Ekwusigo: ADC – 261 | APC – 2,973 | APGA – 18,749 | PDP – 70

Idemili ta Kudu: ADC – 213 | APC – 6,015 | APGA – 17,224 | PDP – 40

Awka ta Kudu: ADC – 1,726 | APC – 5,038 | APGA – 27,896 | PDP – 63

Anambra ta Yamma: ADC – 152 | APC – 3,428 | APGA – 9,318 | PDP – 102

Ihiala: ADC – 135 | APC – 4,425 | APGA – 23,557 | PDP – 69

Jami'ar INEC ta suma a zaben Anambra

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata jami’ar INEC ta yanke jiki ta sume a yayin zaben gwamnan Anambra saboda hayaniya da matsalar na’urar BVAS.

An samu rahoto cewa dubban masu jefa kuri’a a Enugwu-Ukwu sun kasa kada kuri’unsu saboda BVAS ta gaza tantance katin masu zabe.

An ce jami’ar, Miss Blessing Egoigwe, ta sume ne yayin da jama’a suka fara hayaniya saboda gazawar na’urar BVAS wajen tantance katin masu zabe da kuma yatsun hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com