Bidiyo: Jami'an EFCC Sun Dura Wurin Zabe a Anambra, An Samu Masu Sayen Kuri'u

Bidiyo: Jami'an EFCC Sun Dura Wurin Zabe a Anambra, An Samu Masu Sayen Kuri'u

  • Jami’an EFCC sun isa Anambra domin sa ido kan yiwuwar sayen kuri’u da kuma tabbatar da gaskiya zaben gwamna
  • An ruwaito cewa an kama wani jami’in jam’iyya yana raka wata mata zuwa rumfar zabe tare da yi mata jagora cikin sirri
  • Ya zuwa yanzu masu sa ido a zaben Anambra sun koka kan yadda ake sayen kuri’a da sauran laifuffuka a wasu yankuna

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra — Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun isa Anambra da safiyar Asabar yayin da jama’a ke fita domin kada kuri’a a zaben gwamna na jihar.

An rahoto cewa jami’an EFCC sun isa makarantar firamare ta CPS da ke Amawbia, karamar hukumar Awka ta Kudu domin sa ido kan zaben da kuma hana sayen kuri’a.

Kara karanta wannan

TAF Africa ta yi magana kan tsaro yayin da ake zaben gwamnan Anambra

An ga zuwan jami'an EFCC yayin da aka yi zargin jami'an jam'iyyun siyasa na sayen kuri'u
Hoton jami'an hukumar EFCC lokacin da suka isa rumfar zabe da ke Amawbia, jihar Anambra. Hoto: Channels TV
Source: UGC

An kama jami’in jam’iyya a Anambra

Sai dai kuma, wani rahoton bidiyo daga Channels TV, ya nuna yadda wata mata a makarantar firamare ta CSU ta shiga rumfar kada kuri’a tare da wani jami’in jam’iyya — abin da ya saba da dokokin zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, an jiyo jami’in jam’iyyar yana tambayarta, “Ego ole?” watau “Nawa kike so?” yayin da yake yi mata jagora.

An ga jami’an zabe na INEC sun garzaya wurin, inda suka zarge shi da keta doka da shiga wurin da ba huruminsa ba, amma ya dage cewa ita ce ta nemi taimako.

Lamarin ya tayar da hankalin jama’a, inda sauran masu kada kuri’a da wakilan jam’iyyu suka nuna rashin amincewa kan hakan, lamarin da ya jawo dan rikici da jinkiri wajen ci gaba da kada kuri’a a rumfar.

Ana fargabar sayen kuri'u a Anambra

Wata mai sa ido daga Situation Room, Dimma Nwobi, ta bayyana cewa sayen kuri’a na gudana a wasu yankuna, musamman a Nnewi ta Arewa, inda ta ce jami’an INEC da ‘yan sanda basu kai kayan zabe wurin cikin lokaci ba.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: Mutanen Anambra sun zabi buga kwallon kafa maimakon kada kuri'a

“Lokacin da muka fito daga Nnewi ta Arewa da misalin 8:15 na safe, mun bar jami'an INEC da ‘yan sanda suna jiran motar da za ta kai su wajen zabe.
"A wasu wuraren kuma, mun ga yadda jam’iyyun siyasa suke karbar katin zaben mutane, suna ba su fom suna cike wa, sannan suna jefa su cikin akwatin zabe,” in ji Nwobi.

- Dimma Nwobi.

Ta kara da cewa wakilan jam’iyyu suna ciniki kai tsaye da masu kada kuri’a, abin da ta kira abin takaici da barazana ga sahihancin zaben.

An ce an ga jami'an jam'iyyun siyasa suna sayen kuri'u a zaben gwamnan Anambra
Wata dattijuwa tana kada kuri'a yayin da ake gudanar da zabe a Najeriya. Hoto: @inecnigeria
Source: Getty Images

Anambra: INEC ta fadi adadin masu zabe

A cewar INEC, akwai masu kada kuri’a 2,802,790 da aka yi wa rajista a jihar, kuma za su kada kuri’a a rumfunan zabe 5,718 da ke cikin kananan hukumomi 21.

Zaben ya shafi daukacin mazabun majalisar dattawa uku na jihar, inda ‘yan takara 16 ke fafatawa don zama gwamna.

Cikin fitattun ‘yan takarar akwai:

  • Gwamna Charles Soludo (APGA)
  • Nicholas Ukachukwu (APC)
  • Paul Chukwuma (YPP)
  • George Moghalu (LP)
  • Jude Ezenwafor (PDP)

'Babu tankardar BVAS a Anambra' - INEC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, INEC ta tabbatar da cewa ta kammala duk shirinta na gudanar da sahihin zaben gwamnan jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Tsakanin APC, APGA: Ƴan Najeriya sun hango wanda zai lashe zaben gwamnan Anambra

Hukumar zaben ta ce ba za a samu wata tangarda da na'urar BVAS ko jinkirin kayan zabe ba, kuma ma'aikata za su isa wurin aikin da wuri.

INEC ta kuma ba da tabbacin cewa ta shirya gudanar da zabe zagaye na biyu idan har babu 'dan takarar da ya cika sharuddan doka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com