"Nan Gaba Za Ku Gode Mini," Gwamna Diri Ya Fadi Asalin Dalilin Ficewarsa daga PDP
- Gwamnan Bayelsa, Douye Diri ya ce ya dauki matakin barin PDP ne saboda maslahar al'ummar jiharsa amma ba kowa zai fahimta ba
- Ana sa ran Gwamna Diri zai shiga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamba, 2025
- Mai girma gwamnan ya shawarci yan siyasa su gujewa gaba a tsakaninsu, su maida hankali wajen inganta rayuwar al'umma
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bayelsa, Nigeria - Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin jam’iyyar PDP saboda maslahar al'ummar jiharsa.
Gwamna Diri ya ce siyasa hanya ce da mutum zai yi wa jama'a hidima kuma ya ba da gudummawa wajen samar da ci gaba.

Source: Facebook
Douye Diri ya fadi haka ne yayin da yake jawabi a taron Thanksgiving wanda aka saba yi duk shekara a cocin Ecumenical Centre da ke Igbogene, Yenagoa, ranar Lahadi, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A watan da ya gabata ne Gwamna Diri ya sanar da ficewarsa daga PDP, kuma ana sa ran zai koma jam'iyyar APC a hukumance ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamba, 2023.
Dalilin Gwamna Diri na barin PDP
Da yake jawabi yau Lahadi, Gwamna Diri ya ce mutanen Bayelsa na da dalilai masu yawa na gode wa Allah saboda zaman lafiya da tsaro da jihar ke ciki a halin yanzu.
Ya jaddada bukatar hadin kai, inda ya shawarci ‘yan siyasa su guji siyasar gaba da fitina, su mayar da hankali kan hadin kai da ci gaban jihar Bayelsa da kasa baki daya.
Gwamna Diri ya ce:
“Wasu daga cikinku ba za su gane ba a yanzu, amma nan da wani lokaci za ku gane kuma ku gode min.
"Wani wani lokacin dole ne mutum ya dauki mataki, kuma na ga wajibi ne a kaina in dauki wannan matakin domin amfanin jihar Bayelsa.”
Ministan Tinubu ya ja hankalin yan siyasa
A nasa jawabin, Karamin Ministan Mai, Sanata Heineken Lokpobiri, ya ja hankalin ‘yan siyasa su rika yin la’akari da sakamakon kowane mataki da za su dauka.
A cewarsa, hadewar Gwamna Diri da gwamnatin tarayya zai amfanar da Bayelsa matuka, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ministan ya gargadi masu nuna rashin biyayya da ladabi ga gwamnan, lamarin da aka ganin kamar shagube ya yi ga mataimakin gwamnan Bayelsa, wanda ya zabi ci gaba da zama a PDP.

Source: Facebook
A nata bangaren, Shugabar Ma’aikatan Tarayya, Dame Didi Walson-Jack, ta ce jihar Bayelsa na da dalilai da dama na gode wa Allah bisa albarkunsa da tagomashin da ya yi wa jihar.
Sanata Agadaga ya bar PDP zuwa APC
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Benson Agadaga mai wakiltar mazabar Bayelsa ta gabas a Majalisar Dattawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mulki.
Sanata Agadaga ya bayyana cewa ya bar PDP ne saboda rikice-rikicen cikin gida da suka lalata jam’iyyar kuma suka rage mata farin jini.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: PDP ta dare gida 2, an dakatar da shugaban jam'iyya na kasa da kan shi
Dan Majalisar Dattawan ya soki PDP da cewa alamarta ta laima ta fashe kuma ta tsage, sannan a cewarsa, jam'iyyar ta rasa mutuncin da take da shi a idon jama'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

