Matasan APC Sun Bukaci Gwamnan Sokoto Ya Nemi Tazarce, an Ji Dalili

Matasan APC Sun Bukaci Gwamnan Sokoto Ya Nemi Tazarce, an Ji Dalili

  • Wata kungiya ta matasan jam'iyyar APC a jihar Sokoto ta bukaci Gwamna Ahmed Aliyu ya sake fitowa takara a zaben 2027
  • Kungiyar ta bayyana cewa gwamnan ya gudanar da ayyukan da ya kamata su sanya ya ci gaba da mulkin jihar a wa'adi na biyu
  • Shugaban kungiyar ya yaba da irin ayyukan ci gaba da gwamnan ya gudanar a lokacin da ya kwashe yana mulkin jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Wata kungiyar matasan jam’iyyar APC mai suna “APC Youth Strategic Alliance for Continuity” ta mika kokon bararta ga Gwamna Ahmad Aliyu.

Kungiyar ta bukaci gwamnan da ya tsaya takarar neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027, saboda salon mulkin da yake gudanarwa.

Matasan APC sun bukaci gwamnan Sokoto ya sake tsayawa takara
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu Sokoto Hoto: Ahmad Aliyu Sokoto
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce shugaban kungiyar, Musa Ladan Sokoto, ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai a ranar Lahadi, 2 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Nentawe: Matasan Arewa sun fadi matsayarsu bayan an fara kiran shugaban APC ya yi murabus

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa 'yan APC ke son ya yi tazarce?

Musa Ladan Sokoto ya ce wannan kira ra’ayi ne na hadin kai daga dubban matasa a fadin jihar da ke ganin cewa wa’adi ɗaya bai wadatar ba don gwamnan ya kammala ayyukan da ya fara.

“Kiranmu ba na siyasar son kai ba ne, amma bisa nasarorin da ake gani da ci gaban da ba za a iya musantawa ba."
"Dakta Ahmad Aliyu ya tabbatar da kansa a matsayin shugaba mai hangen nesa wanda yake gina sabuwar Sokoto, mai zaman lafiya, haɗin kai, da ci gaba."

- Musa Ladan Sokoto

Ya ce a karkashin gwamnatin yanzu, kowace karamar hukuma a jihar tana da akalla wani aiki da ke gudana ko wanda aka kammala, daga hanyoyi, makarantu, asibitoci, ruwa, har zuwa wutar lantarki.

Gwamna Ahmad Aliyu ya samu yabo

Dangane da walwalar ma’aikata, kungiyar ta yabawa gwamnan bisa aiwatar da tsarin sabon mafi karancin albashi, biyan albashi a kan lokaci, da kuma biyan bashin fansho da hakkokin tsofaffin ma’aikata.

Kara karanta wannan

ADC ta samu karuwa a Kano, tsohon dan majalisa ya fice daga APC zuwa jam'iyyar

Haka kuma, kungiyar ta yabawa jajircewar gwamnan ga cibiyoyin addini ta hanyar biyan alawus ga limamai da na’ibai, tare da tallafawa ilimin addinin Musulunci a fadin jihar.

A fannin tsaro, Musa Ladan ya ce gwamnan ya karfafa rundunar tsaro ta jihar, ya inganta haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, tare da samar da karin kayan aiki don yakar ‘yan ta’adda da sauran laifuffuka, rahoton Tribune ya tabbatar da labarin.

Kungiyar ta kuma jaddada cewa shirin gwamnan na sauya fasalin jihar ya haɗa da inganta rayuwar matasa, ‘yan kasuwa, da masu sana’o’i musamman a matakin kananan hukumomi.

Matasan APC sun bukaci gwamnan Sokoto ya sake fitowa takara
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, da aka bukaci ya sake fitowa takara Hoto: Ahmad Aliyu Sokoto
Source: Facebook
“A matsayin girmamawa da biyayya, mu matasan jihar Sokoto mun yanke shawarar sayawa Mai girma gwamna fom ɗin takara idan lokacin ya yi. Wannan ne hanyarmu ta nuna godiya da goyon baya."

- Musa Ladan Sokoto

A karshe, kungiyar ta sake yin alkawarin ci gaba da goyon bayan gwamnan tare da yin aiki tare da gwamnatinsa domin gina Sokoto mai zaman lafiya, ci gaba, da haɗin kai ga kowa da kowa.

An yi watsi da kiran shugaban APC ya yi murabus

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar matasan Arewacin Najeriya mai suna Northern Nigeria Youth Leaders Forum (NNYLF), ta yi watsi da kiran shugaban jam'iyyar APC na kasa ya yi murabus daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: PDP ta dare gida 2, an dakatar da shugaban jam'iyya na kasa da kan shi

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa masu bukatar Farfesa Nentawe Yilwatda ya yi murabus daga mukaminsa ba 'yan jam'iyyar APC ba ne.

Ya nuna cewa shugaban na APC ya yi kokari sosai tun bayan mukamin da aka ba shi na jagorancin jam'iyyar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng