ADC Ta Samu Karuwa a Kano, Tsohon Dan Majalisa Ya Fice daga APC zuwa Jam'iyyar
- Jam'iyyar APC ta rasa daya daga cikin manyan 'yan siyasan da suka kasance a cikinta tun lokacin kafuwarta a jihar Kano
- Tshon dan majalisar wakilai, Hon. Nasiru Baballe Ila, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulki
- Hon. Nasiru Baballe wanda ya taba zama hadimin marigayi Muhammadu Buhari, ya koka kan yadda aka rika nuna masa wariya a APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Tsohon ɗan majalisa kuma tsohon mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin majalisar wakilai, Hon. Nasiru Baballe Ila, ya sanar da ficewarsa daga APC.
Nasiru Baballe Ila ya fice daga APC ne saboda abin da ya kira rashin adalci da rashin dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyar.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta rahoto cewa ya bayyana hakan ne a wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 23 ga Oktoba 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasiru Baballe ya fice daga APC
Ya aika wasikar ne ga shugaban jam'iyyar APC na gundumar Gyadi-Gyadi ta Arewa a karamar hukumar Tarauni ta jihar Kano.
Nasiru Baballe Ila ya bayyana matakin nasa na yin murabus daga APC a matsayin shawara mai radadi amma wadda ta zama dole.
Ya zargi shugabancin jam’iyyar da watsi da tsofaffin ’yan jam’iyya, musamman wadanda suka fito daga tsohuwar CPC, ɗaya daga cikin jam’iyyun da suka haɗu suka kafa APC.
“Yadda aka mu’amalance ni a cikin jam’iyyar, musamman a Kano, da wasu abubuwa masu muhimmanci da suka faru, sun tilasta mini ɗaukar wannan mataki."
- Hon. Nasiru Baballe Ila
Meyasa ya rabu da jam'iyyar APC?
Nasiru wanda ya wakilci mazabar Tarauni a majalisar wakilai tsakanin 2011 da 2019, ya koka cewa duk da irin jajircewarsa ga jam’iyyar tun daga kafuwarta, ana ci gaba da nuna masa wariya da magoya bayansa ba tare da la’akari da gudunmawarsu ba.
“Baya ga abin da nake fuskanta ni da magoya bayana, rashin amincewa da shigar da mu, waɗanda muka fito daga CPC cikin muhimman harkokin jam’iyya, abu ne mai tada hankali."
- Hon. Nasiru Baballe Ila
Ya kuma tuna yadda aka ki ba shi tikitin takara domin sake komawa majalisa a zaben 2019, abin da ya ce ya nuna yadda jam’iyyar ke kaucewa adalci da haɗin kai.
“Rashin dimokuraɗiyya da haɗin kai a cikin jam’iyyar ya sabawa ainihin akidun da ta ke da su a matsayin jam’iyya mai ra’ayin ci gaba."
"A matsayina na mutum mai gaskiya da ka’ida, ba zan iya ci gaba da kasancewa cikin jam’iyya da ta saba da dabi’u na ba."
- Hon. Nasiru Baballe Ila

Source: Facebook
Ya koma jam'iyyar ADC
Tsohon mai taimaka wa shugaban kasan, wanda ya yi aiki a karkashin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar ADC, inda ya ce za a mutunta dabi’u da akidunsa.
“Bayan nazari mai zurfi, na yanke shawarar haɗa kai da sabuwar jam'iyyar da ke wakiltar ainihin dalilin da ya sa na shiga siyasa, wato hidima ga jama'a."
- Hon. Nasiru Baballe Ila
Ya kara da cewa zai ci gaba da bin siyasar lumana ba tare da gaba ba.
Mambobin PDP sun koma APC a Enugu
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan majalisar wakilai na jam'yyar PDP sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyar.
'Yan majalisar wakilan guda biyar sun koma jam'iyyar APC mai mulki bayan sun raba gari da PDP.
Sun bayyana cewa sun dauki matakin ne saboda rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar PDP wanda ta kasa magancewa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


