Trump Na Barazana ga Najeriya, Minista Ya Cika Baki kan Tazarcen Tinubu a 2027

Trump Na Barazana ga Najeriya, Minista Ya Cika Baki kan Tazarcen Tinubu a 2027

  • Ministan harkokin cikin gida, Olabunmi Tunji-Ojo ya yi tsokaci kan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Olabunmi Tunji-Ojo wanda ya yi magana ta hannun kungiyarsa ya nuna cewa Shugaba Tinubu zai sake darewa kan kujerarsa cikin sauki
  • Ministan ya bayyana cewa yunkurin da 'yan adawa ke yi na yi masa taron dangi a zaben 2027, ba zai yi nasara ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ministan harkokin cikin gida, Olabunmi Tunji-Ojo, ya yi magana kan tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa babu irin adawa ko haɗin gwiwar siyasa da za ta iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu samun nasara a zaben shekara ta 2027.

Tunji Ojo ya magantu kan tazarcen Shugaba Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Olabunmi Tunji-Ojo Hoto: @DOlusegun, @BTOfficial
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce Olabunmi Tunji-Ojo, ya bayyana hakan ne ta hannun kungiyarsa ta goyon baya, BTO for PBAT, a ranar Asabar, 1 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya dora alhakin kisan Kiristoci a Najeriya kan Jonathan a 2014

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Minista ya ce kan tazarcen Tinubu?

Ministan ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da manufofin cigaba da shugaban kasar ke aiwatarwa sun sanya takararsa ta wa’adi na biyu ta samu babban tagomashi.

Da yake jawabi a madadin ƙungiyar, Folajimi Adewumi ya bayyana cikakken amincewa da jagorancin Tinubu da kuma shirye-shiryen jam’iyyar APC wajen ci gaba da rike mulki.

“Babu wanda zai iya hana Shugaba Tinubu lashe zaben 2027. Sai dai idan ba a yi zabe ba a Najeriya, ko kuma idan shugaban kasa da kansa ya ƙi sake tsayawa takara."
"Babu wani abin da zai hana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu samun nasara a 2027."

- Folajimi Adewumi

Ya sake nanata cewa kungiyar BTO for PBAT 2027 ta yi yawon ganin halin da ake ciki a sassan kasar don tantance ra’ayin jama’a da kuma nuna irin nasarorin da gwamnatin ke samu.

“Mun gani da idanunmu yadda manufofin Shugaba Tinubu ke haifar da tasiri mai kyau wajen gina ababen more rayuwa, tabbatar da tsaro da aiwatar da gyaran tattalin arziki."

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani bayan Tinubu ya sassauta hukuncin Maryam Sanda

"'Yan Najeriya sun fara ganin sakamako, kuma zuwa 2027, za a tabbatar da manufar Renewed Hope."

- Folajimi Adewumi

Tunji Ojo ya ce Tinubu zai yi tazarce a 2028
Ministan harkokin cikin gida, Olabunmi Tunji-Ojo Hoto: @BTOfficial
Source: Facebook

APC ta koyi darasi a 2023

A nasa bangaren, shugaban kungiyar, Ogbeni Adojutelegan Adesuyi, ya ce jam’iyyar APC ta koyi darussa masu muhimmanci daga zaben 2023.

Ya ce APC ta yi nazari sosai kan kura-kuranta, musamman a jihohin Legas da Kano, sannan ta farfado da tsarin ta don karfafa tushen jam’iyyar a matakin jama’a.

Tinubu ya tarbi jiga-jigan PDP zuwa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tarbi manyan 'yan siyasa da suka sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC a Kudancin Kaduna.

Manyan 'yan siyasan sama da guda 10 da suka sauya sheka sun hada da 'yan majalisar tarayya da na jihohi tare da dumbin magoya bayansu.

Shugaba Tinubu Ya yaba wa Gwamna Uba Sani saboda irin jagorancinsa na haɗin kai, yana mai kira gare shi da ya ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa jam’iyyar APC a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng