PDP Ta Dare Gida 2, An Dakatar da Shugaban Jam'iyya Na Kasa da Kan Shi

PDP Ta Dare Gida 2, An Dakatar da Shugaban Jam'iyya Na Kasa da Kan Shi

  • Rikicin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ya kara daukar zafi bayan an samu wani bangaren da ya balle daga cikinta
  • Sabon bangaren wanda ke goyon bayan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya dakatar da shugaban jam'iyyar na kasa
  • Hakazalika an kuma dakatar da wasu mambobin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC), tare da tura su zuwa gaban kwamitin ladabtarwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta dare gida biyu bayan da aka samu wani bangare da ke goyon bayan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Tsagin na PDP ya sanar da dakatar da shugaban rikon kwarya na jam’iyyar, Umar Damagum, da wasu mambobin kwamitin gudanarwa na kaaa (NWC) guda biyar.

An dakatar da shugaban PDP na kasa
Sanata Samuel Anyanwu tare da sauran mambobin tsagin PDP Hoto: @ImranMuhdz
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce sakataren PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Asabar, 1 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya dauki sabon salo, an dakatar da manyan shugabannin jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar PDP ta rabu gida 2

Vanguard ta ce Samuel Anyanwu, wanda ya yi magana a madadin bangaren NWC na Wike, ya bayyana cewa mataimakin shugaban jam’iyya na kasa (Arewa ta Tsakiya), Mohammed Abdulrahman, zai zama sabon shugaban rikon kwarya na PDP.

“Abin takaici ne wasu su ce an dakatar sakataren jam'iyya na kasa da sakataren tsare-tsare na kasa wadanda ke da alhakin lura da dukkan harkokin jam’iyya, da Lauyan jam’iyya na kasa."
"A kan haka, mun yanke shawarar dakatar da shugaban jam'iyya na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagum, saboda rashin iya jagoranci, almundahana, da kin bin hukuncin kotu. An dakatar da shi na tsawon wata guda, kuma zai fuskanci kwamitin ladabtarwa."
"Haka kuma, mun dakatar da mai magana da yawun jam’iyya na kasa, Debo Ologunagba, saboda yawan fitar da sanarwa ba tare da amincewar jam’iyya ba. Mataimakin Shugaban jam’iyya na kasa (yankin Kudu), Taofeek Arapaja, shi ma an dakatar da shi."

Kara karanta wannan

"Babu abin da za mu fasa," Jam'iyyar PDP ta yi magana bayan hukuncin kotu

"An dakarar sakataren kudi na kasa, Daniel Woyenguikoro, wanda ake zargi da aikata almundahana ta kudi"
"Hakazalika an dakatar shugaban matasa Sulaiman Kadade, da mataimakin sakatare na kasa, Setonji Koshoedo, na tsawon kwanaki 30, kuma za su fuskanci kwamitin ladabtarwa domin su bayyana dalilin da ya sa ba za a kore su gaba daya daga jam’iyya ba."
"Muna sanar da cewa mataimakin shugaban jam'iyya na kasa (Arewa ta Tsakiya), Mohammed Abdulrahman zai ci gaba da zama shugaban rikon kwarya na jam’iyya."

- Sanata Samuel Anyanwu

Jam'iyyar PDP ta rabu gida biyu
Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Umar Iliya Damagum Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

An dakatar da Anyanwu daga PDP

Sai dai kafin wannan sanarwa, Majalisar NWC ta riga ya dakatar da Sanata Samuel Anyanwu, tare da lauyan jam’iyya na Kasa, Kamaldeen Ajibade (SAN), da wasu mambobi biyu.

Hakan na nuna cewa jam’iyyar PDP ta fada cikin rikici mai zafi tsakanin jagorancin Damagum da mutanen Wike.

Kotu ta hana babban taron PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotu ta kawo cikas ga shirin jam'iyyar PDP na gudanar da babban taronta na kasa.

Kara karanta wannan

Kotu ta jikawa PDP aiki, ta dakatar da babban taron jam'iyyar na kasa

Babbar kotun tarayya wadda ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ya dakatar da jam'iyyar PDP daga gudanar da babban taronta na kasa.

Alkalin kotun, mai shari'a James Omotosho, ya bada wannan umarnin yayin yanke hukunci kan wata kara da wasu mambobin jam'iyyar suka shigar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng