APC Ta Bankado Shirin Kai wa Shugaban Jam'iyya, Nentawe Yilwatda Hari a Filato

APC Ta Bankado Shirin Kai wa Shugaban Jam'iyya, Nentawe Yilwatda Hari a Filato

  • Jam’iyyar APC ta bayyana cewa an kulla makirci don kai wa Shugabanta na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, hari a Gindiri, Jihar Filato
  • Sakataren jam’iyyar ya ce an riga an tanadi ‘yan daba da motocin da za su kai su wajen taron tsofaffin daliban Gindiri a ranar Lahadi
  • APC ta bukaci jami’an tsaro su binciki lamarin don hana tashin hankali da tabbatar da tsaro yayin ziyarar shugabanta na kasa a Filato

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Jam’iyyar APC a jihar Filato ta yi ikirarin cewa wasu mutane na shirin kai hari kan Shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda.

Ta ce za a kai harin ne a lokacin taron tsofaffin daliban makarantar Gindiri da za a gudanar a ranar Lahadi, 2 ga Nuwamba, 2025, a garin Gindiri, karamar hukumar Mangu.

Kara karanta wannan

Yadda aka sace mataimakin shugaban majalisar Kebbi bayan fita daga sallah a masallaci

Nentawe Yilwatda
Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa an bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai rikon mukamin sakataren yada labaran jam’iyyar na jihar, Shittu Bamaiyi, ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta bayyana cewa ta gano bayanan sirri kan makircin da aka kulla domin cin zarafin shugaban jam’iyyar.

The Sun ta ce sanarwar ta ce an shirya taron a wani gida mai zaman kansa a Jos inda masu daukar nauyin harin ke kammala shirye-shiryen karshe.

APC ta ce za a kaiwa shugabanta hari

Bamaiyi ya bayyana cewa bisa ga bayanan da jam’iyyar ta samu, an tanadi motocin haya guda uku a mazabu 20 da ke cikin karamar hukumar Mangu domin jigilar ‘yan daba zuwa wajen taron.

“An shirya su, an kai su Gindiri, inda taron tsofaffin daliban Gindiri zai gudana, da nufin bata sunan shugaban jam’iyyar da tawagarsa,”

- Inji sanarwar

Ya kara da cewa, rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun nuna cewa wasu ‘yan daba za su tsaya a Gindiri, inda za su rika ihu da cewa, ‘Ba ma so! Ba ma so!’ da zarar Nentawe ya isa garin.

Kara karanta wannan

Hotunan 'yar takarar gwamna sun jijjiga kafar sadarwa, ta bayyana surar jikinta

Nentawe Yilwatda
Nentawe Yilwatda tare da wasu 'yan APC. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

Bamaiyi ya ce an shirya yadda ‘yan jarida daga cikin da wajen Jihar Filato za su kasance a wurin domin yada hotuna da rahotannin da za su nuna kamar mutanen jihar ba sa son Nentawe.

Kiran APC ga jami'an tsaron Filato

Jam’iyyar APC ta bayyana damuwarta cewa wannan makirci zai iya haifar da tashin hankali a jihar, don haka ta bukaci jami’an tsaro da su gaggauta gudanar da bincike domin gano masu hannu a ciki.

“Ina kira ga hukumomin tsaro da su binciki wannan batu da gaggawa, domin tabbatar da cewa ba a kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ba,”

- Inji Bamaiyi

Gwamna Diri zai koma jam'iyyar APC

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya kammala shirin komawa jam'iyyar APC mai mulki.

Ana rade-radin cewa a makon farko na Nuwamban 2025 ne gwamna Diri zai fice daga PDP zuwa jam'iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

'Za su rika gudu,' Sabon shugaban sojan sama ya fadi yadda zai birkita 'yan ta'adda

Hakan na zuwa ne yayin da gwamnoni, musamman na PDP da 'yan majalisu ke barin jam'iyyunsu suna komawa APC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng