Rajistar Jam'iyyu: INEC Ta Fadi Kungiyoyi 8 da Suka Tsallake zuwa Mataki na Gaba
- Hukumar INEC ta tabbatar da cewa ƙungiyoyi takwas ne suka kammala matakin farko na neman zama jam’iyyu a Najeriya
- Rahotanni sun nuna cewa kungiyoyi shida sun fadi a matakin saboda rashin cika ka’idojin da hukumar INEC ta tanada
- INEC ta ce za ta ci gaba da nazarin takardun da aka tura domin tabbatar da bin dokokin ƙasa da na zaɓe kan rajistar jam'iyyu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar zabe ta INEC ta bayyana cewa ƙungiyoyi takwas ne kacal daga cikin 14 da aka tantance a baya suka kammala matakin farko na neman rajista a matsayin jam’iyyun siyasa.
A cewar hukumar, an ki amincewa da ƙungiyoyi shida saboda rashin bin ƙa’idoji da cikakken bayanai kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan
Sojoji sun kama karin mutane 26 da ake zargi da hannu a shirya yi wa Tinubu juyin mulki

Source: Twitter
Legit Hausa ta tattaro bayanan da hukumar INEC ta yi ne a cikin wani sako da aka wallafa a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan INEC mai kula da harkokin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Sam Olumekun ne ya sanya hannu kan takardar.
Olumekun ya tunatar cewa hukumar ta fara wannan aiki tun daga 17, Satumba, 2025, inda aka bai wa ƙungiyoyi damar mika takardunsu daga 18 ga Satumba zuwa 18 ga Oktoba, 2025.
Kungiyoyin da suka cika sharudan INEC
A cewar INEC, cikin ƙungiyoyi 14 da aka amince da su a baya, takwas ne suka kammala samar da dukkan takardu da bayanan da ake buƙata kafin ƙarewar wa’adin ranar 19, Oktoba, 2025.
Sanarwar ta ce:
“A ranar Asabar, 19, Oktoba, 2025, ƙungiyoyi takwas daga cikin 14 sun kammala shigar da bayanan su da takardun da ake buƙata.”
Punch ta wallafa cewa kungiyoyin da suka cika sharudan sun haɗa da ADA, CDA, ASP, AAP, DLA, GFP, NDP, da PFP.

Kara karanta wannan
'Za su rika gudu,' Sabon shugaban sojan sama ya fadi yadda zai birkita 'yan ta'adda
Matakin na gaba wajen tantance kungiyoyin
INEC ta bayyana cewa mataki na gaba zai kasance ne na cikakken nazari da tantance bayanan kungiyoyin.

Source: Twitter
Hukumar ta ce za a yi haka ne domin tabbatar da cewa dukkan bayanan da ƙungiyoyin suka gabatar sun dace da kundin tsarin mulkin 1999, dokar zaɓe ta 2022, da ƙa’idojin INEC.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“Mataki na gaba shi ne yin cikakken tantancewa domin tabbatar da bin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, dokar zaɓe ta 2022, da kuma ƙa’idojin INEC na 2022 don rajistar jam’iyyu.”
A baya, hukumar ta karɓi wasiku 171 daga ƙungiyoyi daban-daban da ke neman samun rajista a matsayin jam’iyyun siyasa, wanda suka ragu zuwa 8 bayan fara tantancewa.
NNPP ya yi magana kan daga zaben 2027
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta yi magana kan neman dawo da zaben 2027 zuwa 2026.
Daya daga cikin jagororin jam'iyyar a Kudu maso Yamma, Olufemi Ajadi ya ce sauya lokacin zabe yana da hadari sosai.

Kara karanta wannan
Tinubu ya cire Maryam Sanda da wasu 'yan safarar kwaya cikin wadanda ya yiwa afuwa
Ya yi magana ne yayin da majalisar dokoki ta fara maganar sauya lokacin domin samun damar kammala shari'o'in bayan zabe kafin shiga ofis.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng