APC Ta Kara Karfi, 'Yan Majalisa 6 daga PDP, LP Sun Koma Jam'iyya Mai Mulki
- Jam'iyyar APC mai mulki ta kara yawan 'yan majalisun da take da su a majalisar wakilan Najeriya
- Wasu 'yan majalisu guda shida na jam'iyyun LP da PDP sun sanar da komawarsu APC a yayin zaman majalisa na ranar Alhamis, 30 ga watan Oktoban 2025
- 'Yan majalisun sun bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da suka ci suka ki cinyewa, sun taimaka wajen yanke shawarar komawa APC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - An samu sabuwar guguwar sauya sheka daga jam'iyyun LP da PDP a majalisar wakilan Najeriya.
'Yan majalisa shida daga jam'iyyun LP da PDP sun sanar da sauya shekarsu zuwa APC a ranar Alhamis, 30 ga watan Oktoban 2025.

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta ce shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya sanar da sauya shekarsu yayin zaman majalisar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar wakilan ya karanta wasikun da suka rubuto domin sanar da sauya shekarsu zuwa jam'iyyar APC
'Yan majalisun LP da PDP sun koma APC
Mutane biyar daga cikin ’yan majalisar da suka sauya sheƙa sun fito ne daga jihar Enugu, yayin da ɗaya ya fito daga jihar Plateau.
Waɗanda suka koma jam’iyyar APC sun haɗa da, Daniel Ago (LP, Plateau), Chidi Obetta (PDP, Enugu), Anayo Onwuegbu (PDP, Enugu)
Sauran sun hada Dennis Agbo (PDP, Enugu), Martins George (PDP, Enugu) da Nnaji Nnolim (PDP, Enugu).
Meyasa suka koma jam'iyyar APC?
Jaridar Tribune ta ce a cikin wasikun da suka aikawa shugaban majalisar, Abbas Tajudeen, sun ce sun bar jam’iyyunsu ne saboda rikice-rikicen cikin gida da suka addabe su.
Bayan sanarwar sauya shekar, an kai su zuwa kujerar shugaban majalisar, inda aka karɓe su a hukumance cikin tafi da murna daga mambobin APC da ke cikin zauren majalisar.
Wannan sabon mataki ya kara zama wani zango na sauya sheƙa zuwa APC da aka sha gani a ’yan makonnin nan, abin da ke nuna yadda jam’iyyar ke ƙara karfafa matsayinta a cikin majalisar wakilai.

Kara karanta wannan
Ba yan ta'adda ba ne: Yan sandan Jigawa sun wanke mutanen da suka shigo da makamai

Source: Facebook
A baya ma, wasu ’yan majalisa daga PDP da LP sun bar jam’iyyunsu saboda rashin kwanciyar hankali da rarrabuwar kawuna da ke cikin waɗannan jam’iyyun.
Sauya shekar ta kuma zo ne a daidai lokacin da ake ganin sabon sauyin siyasa a sassa daban-daban na kasar nan, musamman a Kudu maso Gabas, inda APC ke kokarin samun gindin zama kafin zaɓen 2027.
Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, da shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, sun halarci zaman majalisar a ranar Alhamis don kallon yadda komawar ta gudana.
Sanatan PDP ya koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta gamu da koma baya a jihar Bayelsa bayan daya daga cikin sanatocin ya sauya sheka.
Sanata Benson Adagada mai wakiltar Bayelsa ta Gabas a majalisar dattawa ya sanar da komawarsa jam'iyyar APC.
Ya bayyana cewa ya dauki matakin sauya shekar ne bayan jam'iyyar PDP ta kasa warware rikice-rikicen da suka addabe ta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
