‘Abin da Zai Faru da Sule Lamido idan Ya Shiga Shari’a da Jam’iyyar PDP’
- Daya daga cikin mambobin kwamitin amintattu na PDP, Bode George ya gargadi Sule Lamido ka da ya kai PDP kotu
- George ya ce daukar matakin da Lamido ke shirin yi na iya jawo masa hukunci daga jam’iyyar idan bai bi hanyoyin da suka dace ba
- Ya ce PDP na son hadin kai ta hanyar amincewar juna, amma hakan ba yana nufin ba a bar wasu ‘ya’ya su tsaya takara ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wani jigo a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Cif Bode George, ya gargadi tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido.
George ya ce Lamido zai iya fuskantar hukunci idan ya kai jam’iyyar kotu kan batun zabensu na shugaban jam’iyyar.

Source: Facebook
George ya bayyana haka ne a hira da shi a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Talata 28 ga watan Oktobar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ya hada Sule Lamido da PDP
Rahotanni sun nuna cewa Lamido ya yi barazanar kai jam’iyyar kotu idan aka hana shi fom din tsayawa takarar shugaban jam’iyya kafin babban taron jam’iyyar.
Tsohon gwamnan ya ziyarci sakatariyar PDP a Abuja don karbar fom, amma an ce sakataren jam’iyya na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, da mai tsara ayyuka Umar Bature, sun ce ba su da masaniyar cewa fom din ya fara fitowa ba.
Kokarin PDP wurin dinke baraka a cikinta
Dattijon ya ce Lamido yana da cikakken ‘yancin tsayawa takarar shugaban jam’iyya, amma bai kamata ya kauce wa hanyoyin sasanta rikice-rikice na cikin gida ba.
“Wannan tsarin ya kasance tun da dadewa a PDP. Idan wasu shugabanni sun yarda su goyi bayan mutum daya a matsayin dan takara na hadin kai, hakan ba yana nufin wasu ba za su iya tsayawa ba.”
- Bode George

Source: Facebook
PDP za ta hukunta Sule Lamido
Goerge ya kara da cewa PDP tana karfafa tattaunawa da hadin kai don guje wa rikici, amma hakan bai hana wani dan jam’iyya tsayawa takara ba.
Sai dai ya yi gargadi cewa duk wanda ya kai jam’iyyar kotu ba tare da ya bi hanyoyin da aka tanada na cikin gida ba, na iya fuskantar ladabtarwa.
Ya kara da cewa:
“Idan kana so ka bi lamari cikin natsuwa, babu matsala. Amma jam’iyya ba ta taba hana kowa tsayawa takara ba.
“Wannan jam’iyya ba mallakin mutum daya ba ce. Kafin ka kai ta kotu, dole ka bi tsarinta. Idan ba ka yi hakan ba, ana iya hukunta ka.”
George ya jaddada cewa Lamido na da ikon neman kujerar, amma idan ya tafi kotu saboda lamarin, zai iya fuskantar hukunci.
Sule Lamido zai hada kan yan Najeriya
Kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya ce PDP za ta dage wajen haɗa kan manyan ‘yan siyasar ƙasar nan domin taimakon jama'a.
Sule Lamido ya bayyana cewa haɗin gwiwar shugabanni daban-daban na siyasa ba don son kai ba ne, sai don kare dimokaradiyya.
Tsohon Gwamnan ya jaddada cewa duk wani dan Najeriya na da hakki ya yi magana don a kawo gyara a yadda ake mulkarsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


