'Yar Takarar Gwamna Ta Yi Alkawarin Biyan Ma'aikata Mafi Karancin Albashin N100,000

'Yar Takarar Gwamna Ta Yi Alkawarin Biyan Ma'aikata Mafi Karancin Albashin N100,000

  • Ana ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra da ke yankin Kudu maso Gabas na tarayyar Najeriya
  • Daya daga cikin 'yan takara ta fito ta gayawa mutanen jihar irin tagomashin da ta shirya musu idan har ta samu nasarar zama gwamna
  • Chioma Ifemeludike ta jam'iyyar AAC ta dauki alkawarin inganta jin dadin ma'aikata ta hanyar kara musu mafi karancin albashi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Anambra - 'Yar takarar jam’iyyar AAC a zaɓen gwamna da za a gudanar a Anambra ranar 8 ga Nuwamba, 2025, Chioma Ifemeludike, ta yi alkawarin inganta walwalar ma’aikata.

'Yar takarar gwamnan ta yi alkawarin kara mafi karancin albashi zuwa N100,000 idan ta lashe zaɓen wanda za a yi a watan Nuwamban 2025.

Ifemeludike ta yi alkawarin kara mafi karancin albashi
Chioma Ifemeludike mai neman kujerar gwamnan Anambra Hoto: @ife_dike
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce 'yar takarar gwamnan ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, inda ta godewa masu shirya taron muhawarar ‘yan takarar gwamna da aka kammala a jihar.

Kara karanta wannan

PDP ta yi wa Sule Lamido martani mai zafi kan barazanar kai ta kara kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yar takarar gwamna ta yi alkawura

Chioma Ifemeludike ta ce wannan ba alkawarin siyasa ba ne, amma kudiri ne na gaske, wanda za a iya cimmawa ta hanyar rage barnar kashe kuɗin gwamnati da kuma zuba jari a harkar noma da habaka hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.

Ta ce taron muhawarar ya bai wa ‘yan takara damar bayyana manufofinsu da kuma kusantar jama’ar Anambra, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar da labarin.

Ifemeludike ta kuma ce kamfen ɗinta na AAC ya fi mayar da hankali kan ƙarfafa matasa da samar da ayyukan yi.

Ta ce gwamnatinta na da shirin zuba jari a fannonin koyar da sana’o’i da horar da matasa kan kasuwanci, domin su samu damar ginawa da kula da nasu kasuwancin.

Ifemeludike ta yi alkawura kan zaben gwamnan Anambra
'Yar takarar gwamnan Anambra, Chioma Ifemeludike Hoto: @ife_dike
Source: Twitter
"Ta hanyar tallafawa matasanmu, za mu rage rashin ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki. Noma muhimmin ginshiki ne kan manufofin da muke son cimmawa."

Kara karanta wannan

Bayan korar mutum 2, APC ta tsaida dan takara a zaben gwamnan Ekiti na 2026

"Za mu zamanantar da noma ta hanyar yin amfani da hanyoyi na zamani da sauya tsofaffin da aka dade ana amfani da su."
"Gwamnatinmu za ta samar tallafin kudi, lamuni da kayan aiki na zamani ga manoma, wanda hakan zai ba su damar samar da amfani mai yawa tare da bada gudunmawa wajen samar da wadataccen abinci da bunkasa tattalin arziki."
“Ta hanyar tallafawa matasa, za mu rage rashin aikin yi kuma mu farfaɗo da tattalin arzikinmu. Noma zai ci gaba da zama ginshikin hangen nesanmu."

- Chioma Ifemedulike

Tsohon dan takara ya daina siyasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar APGA a zaben 2023, Farfesa Farfesa Peter Umeadi, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar.

Farfesa Peter Umeadi ya bayyana cewa ya jingine duk wani abu da ya danganci siyasa, wanda hakan ke nufin babu ruwansa da batun siyasa a Najeriya.

Tsohon alkalin yana daya daga cikin yan takarar da suka fafata da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinhbu a zaben 2023.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng