Bayan Korar Mutum 2, APC Ta Tsaida 'Dan Takara a Zaben Gwamnan Ekiti na 2026
- Jam'iyyar APC ta ayyana Gwamna Biodun Oyebanji a matsayin dan takararta a zaben gwamnan jihar Ekiti da za a gudanar a 2026
- Oyebanji ya samu wannan nasara ne bayan gaba daya masu zaben 'dan takara sun kada masa kuri'a a zaben fitar da gwani a Ado-Ekiti
- Wannan ya ba gwamnan damar neman tazarce a kan mulki a zaben jihar Ekiti da INEC shirya yi ranar 2 ga watan Yuni, 2025
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ado-Ekiti, Najeriya – Gwamnan Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben da za a gudanar ranar 20 ga Yuni, 2026.
Hakan na zuwa ne bayan deleget watau masu zaben 'dan takara na APC sun amince da Gwamna Oyebanji a matsayin dan takarar masalaha.

Source: Facebook
Gwamna Oyebanji ya samu kuri'u 885
The Nation ta ce Oyebanji, wanda shi ne kaɗai ɗan takara a zaben fitar da gwanin, ya samu kuri’un deleget 885, mutum biyar daga kowace mazaba daga cikin mazabu 177 na jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gaba daya deleget din sun marawa Gwamna Oyebanji baya ne biyo bayan janyewar Misis Atinuke Oluremi Omolayo daga takara.
APC ta kori mutum 2 daga takara
Tun farko APC ta cire Kayode Ojo da Abimbola Olajumoke daga jerin masu takara, saboda ba su cika ka’idoji ba, wanda hakan ya so tayar da kura a jam'iyya mai mulki.
Misis Omolayo, wacce ta tsallake tantancewar da kwamitin APC ya gudanar kwanakin baya, a janye a hukumance a wurin taron fitar da gwanin da aka gudanar a Ekiti Parapo Pavilion, Ado-Ekiti yau Litinin.
Ta bayyana cewa ta yanke shawarar hakan ne saboda nagartar aikin Gwamna Oyebanji da kuma kokarinsa wajen ci gaban jihar Ekiti tun da ya hau karagar mulki.
A cewarta:
“Gwamna Oyebanji ya yi aiki sosai. Ayyukansa a fannoni daban-daban kamar gine-gine, shugabanci da hada kan al’umma sun isa hujja, ya cancanci wa’adi na biyu, shi yasa na janye domin goyon bayansa.”
Ta kuma rushe tsarin siyasar ta a kananan hukumomi 16 na jihar domin ta tallafa wa sake zaben Oyebanji, tana mai cewa janyewarta alama ce ta biyayya ga jam’iyya da kishin ci gaban Ekiti.

Source: Facebook
Yadda aka zabi dan takarar APC a Ekiti
Bayan janyewar ta, Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya gabatar da kudirin amincewa da Oyebanji a matsayin ɗan takarar gwamna na APC.
Kuma nan take, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ekiti, Adeoye Aribasoye, ya goya masa baya bisa sashe na 84(11) na dokar zabe ta 2022, kamar yadda Leadership ta rahoto
Daga nan aka ba da damar kada kuri’ar murya kuma duka deleget suka amsa da “eh!”, wanda hakan ya tabbatar da Gwamna Oyebanji a matsayin ɗan takarar APC a zaben gwamna na 2026.
Gwamnan Ekiti ya sallami kwamishinoni
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya sallami wasu dava cikin kwamishinoni da jami'an gwamnatinsa.
Gwamna Biodun Oyebanji ya sanar da rusa Majalisar Zartarwa ta jihar Ekiti yayin da zaben gwamna ke kara karatowa.
Korar da aka yi ta shafi wasu kwamishinoni da manyan masu ba da shawara na musamman ga Gwamnatin Biodun Oyebanji.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


