APGA: Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Jingine Siyasa Gaba Daya a Najeriya

APGA: Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Jingine Siyasa Gaba Daya a Najeriya

  • Tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar APGA, Farfesa Peter Umeadi ya bayyana cewa ya jingine siyasa gaba daya
  • Farfesa Umeadi, wanda ya kara da Shugaba Tinubu a zaben 2023 ya tabbatar da haka ne a wata wasika da ya aikawa shugaban APGA
  • Ya sanar da APGA cewa ya bar jam'iyyar kuma ba zai sake shiga duk wata mu'amala ta siyasa ba daga ranar 24 ga Oktoba, 2025

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Awka, Anambra – Farfesa Peter Umeadi, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar APGA a zaben 2023, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Jagororin PDP sun rabu a kan bai wa turaki shugabancin jam'iyya

Farfesa Umeadi, tsohon alkali ya kuma bayyana cewa ya jingine siyasa gaba daya, watau ya janye kansa daga duk wata mu’amala ta siyasa a Najeriya.

Farfesa Peter Umeadi.
Hoton tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar APGA, Farfesa Peter Umeadi Hoto: @Me_lordd
Source: Twitter

Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika da ya rubuta da hannunsa, ya aika wa shugaban APGA na gundumar Nri Ward 1 da ke jihar Anambara, Onyekwelu Jideobi, in ji Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Umeadi ya fice daga APGA

Wasikar mai dauke da kwanan watan 24 ga Oktoba, 2025, ta ce:

“na rubuto wannan wasika cikin girmamawa domin sanar da ficewata daga jam’iyyar APGA a mazabar Nri Ward 1.
"Haka kuma, na janye kaina daga duk wata siyasa a Najeriya. Ina gode wa APGA saboda damar da ta bani na zama dan takararta a zaben shugaban ƙasa na 2023.
"Ficewata daga jam’iyyar APGA da kuma janyewata daga siyasa ya fara aiki daga yau. Da fatan za ku karɓi sakon gaisuwata cikin girmamawa.”

Farfesa Umeadi, wanda ya nemi mulki tare da abokin takararsa, Mohammed a tikitin Umeadi/Mohammed 2023, shi ne mutumin farko daga fannin shari’a da ya tsaya takarar shugaban ƙasa karkashin babbar jam’iyya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon 'dan takarar shugaban kasa a APC ya raba man fetur kyauta ga jama'a

Yadda Umeadi ya nemi takara a 2023

Manufar kamfen ɗinsa ta ta’allaka ne kan mulki bisa tsarin doka, raba iko tsakanin sassan gwamnati, da bin ka’ida, tare da kawo ci gaban zamantakewa da daidaito ga ’yan Najeriya.

Tsohon alkalin yana daya daga cikin yan takarar da suka fafata da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinhbu a zaben 2023, kamar yadda Punch ta kawo.

Jam'iyyar APGA.
Hoton tambarin jam'iyyar APGA. Hoto: OfficialAPGA
Source: Twitter

Umeadi ya shiga jam’iyyar APGA a ranar 20 ga Maris, 2019, a gundumar Nri Ward 1, kuma ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a ranar 1 ga Yuni, 2022.

An haifi Mai Shari’a Umeadi (Mai ritaya) a ranar 4 ga Yuli, 1955. Ya taɓa zama Babban Alkalina Jihar Anambra daga 2011 zuwa 2019.

Wani mataahin dan siyasa a jihar Katsina, Hon. Sani Abdullahi Ahmad ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan mataki da tsohon dan takarar ya dauka ya yi daidai.

A cewarsa, lokaci ya yi da tsofaffin yan siyasar nan za su kauce su ba matasa damar mulkin kasar nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada sabon minista, ya aika suna ga majalisar dattawa domin tantancewa

"Ni ya burge ni, idan mutum ya manyanta ko a siyasa ne ya kamata ya nuna cewa ya girma, matasa sun cancanci a basu dama su jagoranci kasar nan," in ji Sani.

ADC ta taso Gwamna Soludo na APGA

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar ADC ta nuna damuwa kan wasu kalaman da ke nuna tayin sayen kuri’a daga bakin gwamnan Anambra.

Rahoto ya bayyana cewa, an zargi gwamna Charles Soludo da kokarin amfani da kudi wajen sayen kuri’a kafin babban zaben gwamna da ke gabatowa a jihar Anambra.

Dokar INEC ta haramta amfani da kudi wajen sayen kuri’a da jan hankalin al’umma a lokutan zabe a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262