Allura ta Tono Garma: An Taso Gwamnan Anambra a Gaba kan Yunkurin Sayen Kuri'a a Lokacin Zabe
- Jam’iyyar ADC ta nuna damuwa kan wasu kalaman da ke nuna tayin sayen kuri’a daga bakin gwamnan Anambra
- Gwamna Charles Soludo ya bayyana cewa, zai ba da kudi ga mazabun da suka zabe shi a zaben gwamna mai zuwa
- Dokar INEC ta haramta amfani da kudi wajen sayen kuri’a da jan hankalin al’umma a lokutan zabe a Najeriya
FCT, Abuja - Mallam Bolaji Abdullahi, sakataren yada labarai na kasa na jam’iyyar ADC, ya bukaci hukumar zabe ta INEC da kada ta yi shiru kan zargin da ake yi wa Gwamna Charles Soludo.
Rahoto ya bayyana cewa, an zargi gwamnan na Anambra da kokarin amfani da kudi wajen sayen kuri’a kafin babban zaben gwamna da ke gabatowa a jihar Anambra.
Abdullahi ya bayyana hakan ne bayan wani jawabi da Gwamna Soludo ya yi a lokacin gangamin yakin neman zabensa a ranar Asabar, inda ya yi alkawarin bayar da kyautar kudi ga kowace mazaba da jam’iyyarsa APGA ta samu nasara a zaben.

Source: Twitter
Bayanan da suka dagawa ADC hankali
A cewar Soludo, wannan tsarin ba sabo ba, domin a baya ma an yi makamancin sa lokacin yakin neman zaben majalisar dattawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce jam’iyyar APGA ta bai wa kowace mazaba da ta ci a lokacin Naira miliyan 1, kuma ta samu nasarar lashe dukkan mazabu a yankin Orumba South.
A cewarsa:
“A lokacin da muke yakin neman zaben majalisar dattawa, mun san cewa za mu lashe dukkan mazabu a Mazabar Sanata ta Kudu, amma duk da haka mun samar da kari.
“Kowace mazaba da APGA ta ci, ta samu Naira miliyan 1, kuma mun lashe dukkan mazabu a Orumba South.”
Ba sabon abu bane sayen kuri’a, inji Soludo
Gwamnan ya kara da cewa wannan al’ada za ta ci gaba da gudana har zuwa babban zaben ranar 8 ga Nuwamba, inda ya sake yin alkawarin kyautar kudi ga mazabu da suka fi samun nasara.
Ya kara da cewa:
“Mun dauki alkawarin biyan kowace mazaba Naira miliyan 1, kuma mako mai zuwa za mu cika alkawarin. A zaben Nuwamba 8, kowace mazaba da ta sake yin nasara za ta samu Naira miliyan 1, yayin da mazabu uku da suka fi yin kokari za su samu Naira miliyan 5, Naira miliyan 2, da Naira miliyan 1 kowacce.”
‘Yan adawa sun kasa natsuwa
Sai dai wannan bayani bai yi wa Mallam Bolaji Abdullahi dadi ba, domin ya bayyana cewa irin wannan magana na nuna cewa Gwamna Soludo ya rasa amincewar jama’ar Anambra.
A cewar Mallam:
“Kafin zaben Nuwamba 8, Soludo ya bayyana a fili cewa ya rasa amincewar mutanen Anambra, kuma hakan ya nuna karara.”
Ya kara da cewa:
“Sai gwamna mai cin ya gama rasa amincewar jama’a ne zai fito fili ya nemi sayen kuri’u da kudi, wanda hakan ya sabawa tanadin sashe na 121 da 127 na Dokar Zabe, wadda ta haramta duk wani nau’in sayen kuri’a.”
Ya kamata INEC ta dauki mataki, jin ADC
Mallam Abdullahi ya kara da cewa irin wannan mataki na nuna rashin kunya da nuna kai tsaye cewa gwamnati ta rasa mutunci a idon jama’a. Ya kuma bukaci INEC da kada ta zura idanu tana ganin abin kamar ba ta sani ba.
Ya bayyana kiransa ga INEC da cewa:
“Wannan sabon mataki ne na kai tsaye wajen nuna rashin kunya da wuce gona da iri, kuma ina fatan INEC ba za ta rufe ido tana ganin abin nan kamar ba ta gani ba.”
Ya ce lokaci ya yi da hukumar zabe za ta tabbatar da adalci da doka a zaben da ke tafe, domin kare mutuncin tsarin dimokuradiyya a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


