Turaki Ya Kara Fuskantar Matsala a Shirin Zama Shugaban PDP Na Kasa
- Jam'iyyar PDP reshen jihar Kebbi ta nuna kin amincewarta da batun takarar tsohon ministan harkoki na musamman, Kabiru Tanimu Turaki
- Mai magana da yawun jam'iyyar ya bayyana cewa ba a tuntube su ba amincewa da Turaki a matsayin dan takarar maslaha don zama shugaban PDP na kasa
- Ta bukaci kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) da ya bar yankin Arewa maso Yamma ya fitar da dan takarar da yake so
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Jam’iyyar PDP a jihar Kebbi ta yi watsi da batun amincewa da Kabiru Tanimu Turaki, a matsayin dan takarar maslaha na shugaban jam'iyyar na kasa.
Jam'iyyar ta ce an dauki matakin ne ba tare da tuntubar shugabannin yankin Arewa maso Yamma ba.

Source: Instagram
Jaridar Daily Trust ta ce mai magana da yawun jam’iyyar PDP a jihar Kebbi, Sani Dododo, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar, 25 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An amince da takarar Turaki
A makon da ya gabata, wasu shugabannin PDP daga Arewa, ciki har da gwamnoni sun amince da Turaki a matsayin dan takararsu domin kujerar shugaban jam’iyyar a babban taron da za a gudanar a watan Nuwamba.
Sai dai Gwamnan Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana bayan taron da aka gudanar a Abuja cewa wannan amincewar ba ta hana sauran ’yan takara tsayawa takara ba.
Me PDP ta ce kan takarar Turaki?
Sani Dododo ya bayyana cewa jam’iyyar a jihar ba ta amince da takarar Turaki ba saboda ba a tuntubi shugabannin yankin Arewa maso Yamma kafin daukar wannan mataki, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
“Matsayar jam’iyyar ita ce a bar yankin Arewa maso Yamma ya zabi dan takararsa domin bin tsarin rabon mukamai na jam’iyyar."
- Sani Dododo
Ya kara da cewa PDP ta jihar Kebbi ta nesanta kanta daga amincewa da Turaki, saboda ba a tattauna da mambobin jam’iyyar a jihar ba kafin a sanya sunansa a cikin jerin ’yan takara.

Source: Facebook
“Mun nesanta kanmu daga wannan abin da muka kira kakaba dan takara daga sama. Dole ne a bar dattawan Arewa maso Yamma su zauna, su tattauna, sannan su fitar da dan takara wanda zai wakilci yankin yadda ya dace."
- Sani Dododo
Sani Dododo ya kuma bukaci kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar da ya bada dama yankin Arewa maso Yamma ya samar da na sa dan takarar na maslaha, domin tabbatar da daidaito da mutuncin tsarin jam’iyyar.
Wike ya ce PDP ta mutu murus
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya yi kalamai kan rikicin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Wike ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta mutu murus sakamakon rashin bin doka da oda da danniya da wasu shugabanninta ke yi.
Ministan ya zargi gwamnonin PDP da wasa da makomar jam’iyyar, yana mai cewa irin yadda suke tafiyar da jam’iyyar, zai kai ta ga rugujewa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

