"An Kawo El Rufa'i," Obasanjo Ya Tona Abin da Ya Faru kafin Yar'adua Ya Zama Shugaban Kasa a 2007

"An Kawo El Rufa'i," Obasanjo Ya Tona Abin da Ya Faru kafin Yar'adua Ya Zama Shugaban Kasa a 2007

  • Cif Olusegun Obasanjo ya ce an ba shi shawarar ya dauki Nasir El-Rufai a matsayin wanda zai gaje shi a 2007 amma ya ki yarda
  • Tsohon shugaban kasar ya ce daga baya ya goyi bayan tsohon gwamnan Katsina, Marigayi Umaru Musa Yar'adua
  • Malam El-Rufai, wanda ya yi gwamna na tsawon zango biyu a Kaduna, na cikin manyan kusoshi a gwamnatin Obasanjo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abeokuta, Ogun State – Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya tuna abin da ya faru lokacin da yake laluben wanda zai ya gaje shi bayan kammala wa'adinsa a 2007.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa wasu gwamnoni da kusoshin Arewa ke son Turaki ya zama shugaban PDP

Obasanjo ya ce an ba shi shawarar ya dauki tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, a matsayin wanda zai gaje shi a mulkin Najeriya amma ya ki yarda.

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Hoton Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo a wurin taro Hoto: Olusegun Obasanjo
Source: Facebook

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa El-Rufai ya yi aiki a gwamnatin Obasanjo, inda ya rike Daraktan Hukumar Sauya Hanyoyin Kasuwanci (BPE) kafin daga bisani ya zama Ministan Abuja daga 2003 zuwa 2007.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin da Obasanjo ke shirin barin mulki a shekarar 2007, ya goyi bayan marigayi Umaru Musa Yar’Adua a matsayin wanda zai gaje shi a fadar shugaban kasa.

Obasanjo ya ki yarda El-Rufai ya gaje shi

Da yake jawabi a Abeokuta, Jihar Ogun, a bikin taron shekara-shekara na Ajibosin Platform mai taken “Muhimmancin Jagoranci a Mulki,” Obasanjo ya tuna abin da ya faru kafin ya zabu Yar'adua.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana yadda tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Osita Chidoka, ya ba shi shawarar ya ɗauki El-Rufai a matsayin magaji, amma ya ƙi.

Chidoka, wanda shi ne babban mai jawabi a taron, ya tuna yadda El-Rufai ya kai ahi wurin Obasanjo lokacin yana da shekaru 34, abin da ya sa ya shiga cikin gwamnati har ya zama Shugaban Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC).

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi garambawul a gwamnatinsa, an sauyawa kwamishinoni ma'aikatu

Me yasa Obasanjo ya ki jawo El-Rufai?

Obasanjo, yayin da yake jawabi, ya yi wa Chidoka magana cikin raha kan yadda ya gaza ba El-Rufai labarin abin da ya faru tsakaninsu, in ji rahoton Channels tv.

Ya ce:

“Ku ji shi fa, bai faɗi wannan ba. A lokacin ina shirin barin mulki, ya zo ya matsa min lamba cewa abokinsa El-Rufai ya kamata ya gaje ni.”

Ya juyo ga Chidoka ya tambaye shi, “ko ba haka ba ne?” Chidoka kuwa ya gyada kai cikin dariya, yana mai tabbatar da maganar.

Cif Obasanjo ya ce ya ƙi aminta da shawarar ne saboda ya ga El-Rufai bai gama girma a siyasa ba.

Obasanjo da Malam El-Rufai.
Hoton tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo tare da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai Hoto: @Elrufai
Source: Twitter

Sai dai Obasanjo ya yaba da irin hazaka da jajircewar Chidoka, El-Rufai, da sauran mutanen da suka yi aiki tare, yana mai cewa irin kwarewar da suka nuna ne ginshiƙin nasarar gwamnatinsa a lokacin.

Sanata Kalu ya karyata Obasanjo

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Orji Uzor Kalu ya zargi tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da yin ƙarya kan ikirarin cewa bai nemi wa’adi na uku ba a mulkinsa.

Kara karanta wannan

Duniya labari: Kwamishina mai ci a Gombe ya yi bankwana da duniya

Kalu ya ce Obasanjo da kansa ya kira shi fadar shugaban ƙasa lokacin yana mulki, ya shaida masa cewa yana da niyyar ƙara wa’adi ta hanyar gyaran kundin tsarin mulki.

Ya ce rikicinsa da Obasanjo ya fara ne bayan ya ƙi goyon bayan wannan shirin, kuma ya sanar da wasu shugabannin ƙasashen duniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262