Gwamna Sule Ya Fallasa Dalilin da Ya Sa Gwamnoni ke Tururuwar Komawa APC
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi tsokaci kan sauya shekar da wasu gwamnoni da wasu 'yan siyasa ke yi zuwa jam'iyyar APC
- Abdullahi Sule ya bayyana cewa sauya shekar da ake gani daga wajen gwamnonin da fitattun 'yan siyasa, na faruwa ne saboda manufofin Bola Tinubu
- Gwamnan ya bayyana cewa manufofin da gwamnatin shugaban kasan ke aiwatarwa na bukatar matukar jarumta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan sauya shekar da gwamnoni da sanatoci ke yi zuwa jam'iyyar APC.
Gwamna Sule ya bayyana cewa shigowar fitattun ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa zuwa APC na faruwa ne sakamakon manufofin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa.

Source: Twitter
Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Lafia, babban birnin jihar, yayin bikin tarbar Sanata Ahmed Wadada wanda ya sauya sheka zuwa APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Ahmed Wadada mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Yamma a majalisar dattawa ya koma jam’iyyar APC daga SDP.
Gwamna Sule ya taya Tinubu murna
“Ina so na taya shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu murna. Saboda irin nagartattun gyare-gyaren da yake kawowa a kasar nan, wadanda ke bukatar jarumta."
"Yanzu duk lokacin da gwamnoni masu ra’ayin cigaba suka hadu, muna tarbar sabon gwamna da ke shigowa jam’iyyarmu."
“A makon jiya mun halarci taro a jihar Kebbi domin tarbar dan uwarmu, Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu, wanda ya koma APC."
"A yayin da muke wurin, wani gwamna ma ya tabbatar da shigowarsa. Da na dawo daga taron, na sake samun labarin wani gwamna ya koma jam’iyyarmu a safiyar yau.”
- Gwamna Abdullahi Sule
Meyasa gwamnoni ke komawa APC?
Gwamna Sule ya ce dalilin dawowar wadannan shugabanni ba don neman lashe zabe ba ne, illa don sun yi amanna da manufofin Shugaba Tinubu na cigaba da gyaran kasa, rahoton New Telegraph ya tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan
Shettima zai taso daga Abuja domin karbar wasu manyan 'yan siyasar Arewa zuwa APC
"Gwamnonin da suke kan mulki suna ganin abin da ke gudana a kasar nan, don haka suna dawowa jam’iyyarmu ba domin zabe ba, sai domin goyon bayan tsare-tsaren Shugaban kasa."
- Gwamna Abdullahi Sule

Source: Facebook
Gwamnan ya kuma yaba wa Sanata Wadada saboda shawarar da ya dauka ta barin SDP don komawa APC.
“Ina taya Sanata Wadada murna. Idan da ya so, da zai iya ci gaba da zama a jam’iyyarsa don ci gaba da kalubalantar mu, amma ya zabi ya shigo cikinmu."
- Gwamna Abdullahi Sule
Gwamna Adeleke ya musanta shirin komawa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Osun, Ademola Nurudeen Jackson Adeleke, ya fayyace zare da abawa kan shirin komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Gwamna Adeleke ya bayyana cewa ko kadan bai da wani shiri na komawa jam'iyyar APC don hadewa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Hakazalika gwamnan ya bada tabbacin ci gaba da zama daram a jam'iyyar PDP, inda ya jaddada cewa suna ci gaba da zaman tattaunawa domin zakulo duk wasu matsaloli tare da magance su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
