Gwamna Uba Sani Ya Yi Albishir ga Tinubu kan Zaben 2027

Gwamna Uba Sani Ya Yi Albishir ga Tinubu kan Zaben 2027

  • Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya halarci wani babban gangamin da aka shirya na jam'iyyar APC mai mulki
  • A yayin gangamin, Gwamna Uba Sani ya karbi mambobin jam'iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC
  • Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa yanzu babu sauran wata adawa a jihar, kuma jam'iyyar APC za ta samu mafi yawan kuri'u a zaben 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi alkawari ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan zaben shekarar 2027.

Gwamna Uba Sani ya yi alkawarin cewa jihar Kaduna za ta ba jam’iyyar APC kaso 95% cikin 100% na kuri’u a zaben shekarar 2027.

Uba Sani ya yi wa Shugaba Tinubu albishir
Gwamna Uba Sani tare da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @ubasanius, @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar The Cable ta ce Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin babban gangamin jam’iyyar APC da aka gudanar a Murtala Square, Kaduna.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin APC ta jawo yunwa da matsalar tsaro a Najeriya, ADC ta fasa kwai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan PDP sun koma APC a Kaduna

A yayin gangamin, ’yan majalisar dokokin jihar guda hudu, ’yan majalisar wakilai guda biyar, da dubban magoya bayansu sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Sauya shekar ya sanya wakilan APC daga jihar Kaduna a majalisar wakilai sun karu zuwa 13, yayin da PDP ta rage da uku.

Haka kuma, a majalisar dokokin jihar Kaduna, APC yanzu tana da mambobi 26, yayin da PDP ke da takwas.

Me Uba Sani ya gayawa Tinubu?

“Ba mu da wata jam’iyyar adawa a Kaduna. Na taba gaya wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu watanni da suka wuce cewa za mu kawo masa kaso 80% cikin 100% na kuri’un Kaduna."
"Amma yau, na sauya matsaya ta, kusan kaso 95% cikin 100% na kuri’un Kaduna za su tafi ga APC a 2027.”

- Gwamna Uba Sani

Gwamnan ya ce yawan sauya sheka zuwa APC ya faru ne sakamakon tsarin mulkinsa na adalci, gaskiya da hadin kai, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan bullo da wani shirin kifar da Tinubu a 2027

Ya kara da cewa jihar Kaduna ce mafi bambance-bambance a Najeriya, amma gwamnatinsa ta yi amfani da wannan bambancin wajen gina zaman lafiya.

“Tun lokacin da muka hau mulki, babu wani rikicin kabilanci ko na addini da ya tashi a Kaduna. Siyasa ita ce hadin kai, talauci kuma baya tambayar addini ko kabila."

- Gwamna Uba Sani

Gwamna Uba Sani ya ce ba adawa a Kaduna
Gwamna Uba Sani yayin gangamin taron APC. Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Uba Sani ya bada tabbaci ga sababbin 'yan APC

Gwamna Uba Sani ya kuma tabbatarwa sababbin mambobin APC cewa za a dauke su daidai da tsofaffin mambobin jam’iyyar.

“Wadanda suka shiga jam’iyyar yau da wadanda suka kafa ta tun farko, dukkansu za su samu dama iri daya."

- Gwamna Uba Sani

Sanatan PDP ya koma jam'iyyar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar Bayelsa ta Tsakiya, Benson Konbowei, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.

Sanata Benson Konbowei ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya bayan ya raba gari da jam'iyyarsa ta PDP.

Ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da suka addabi PDP na daga cikin dalilan da suka sanya ya fice daga jam'iyyar wadda ya lashe zabe a karkashinta a shekarar 2023.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng