Tsugune ba Ta Kare ba: Gwamna na Iya Rasa Kujerarsa bayan Barin PDP da Ta Kawo Shi

Tsugune ba Ta Kare ba: Gwamna na Iya Rasa Kujerarsa bayan Barin PDP da Ta Kawo Shi

  • Lauyoyi sun rabu kan halaccin Gwamna Douye Diri na ci gaba da mulki bayan ficewa daga jam’iyyar PDP ba tare da shiga sabuwa ba
  • Wasu lauyoyi suna cewa ficewarsa daga PDP bai sabawa doka ba, yayin da wasu ke cewa hakan na iya sa ya rasa mukaminsa
  • Lauyoyi kamar Monday Ubani da Abiodun Olatunji sun ce kundin tsarin mulki bai tanadi cewa ficewa daga jam’iyya na kawo cire gwamna ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yenagoa, Bayelsa - An taso Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri bayan yin murabus daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

Murabus din nasa ya janyo cece-kuce tsakanin lauyoyi bayan ya fice daga PDP da ta kawo shi mulki ba tare da shiga sabuwar jam’iyya ba.

An taso gwamna a gaba bayan barin PDP
Gwamna Douye Diri na Bayelsa ya yi murabus daga PDP. Hoto: Douye Diri.
Source: Facebook

Lauyoyi sun magantu kan kujerar Gwamna Diri

Kara karanta wannan

ADC ta yi babban kamu, tsohon shugaban PDP ya yi murabus bayan shekaru 22

Rahoton Arise News ya ce lauyoyi sun bayyana cewa hakan ya saba wa tsarin mulki, suna masu cewa Diri ya rasa cancantar ci gaba da zama gwamna bayan ficewar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai wasu sun dage cewa babu doka da ta ce dole ne gwamna ya ci gaba da kasancewa dan jam’iyya bayan an rantsar da shi.

Babban Lauya, John Olusola Baiyeshea (SAN), ya ce dole Diri ya shiga wata jam’iyya domin babu tsarin ‘yan takara masu zaman kansu a Najeriya.

Ya gargade shi cewa, idan bai shiga sabuwar jam’iyya cikin gaggawa ba, masu adawa na iya kai shi kotu domin a cire shi daga kujerarsa.

Sai dai ya kara da cewa ko da hakan na iya zama dalilin tsigewa, yiwuwar hakan ta yi wuya saboda ‘yan majalisar jihar da suka yi murabus tare da shi.

Wani lauya, Eko Ejembi Eko (SAN), ya bayyana cewa tun da PDP ce ta lashe zabe, gwamnan bai kamata ya kasance ba tare da jam’iyya ba.

Lauyoyi sun rarrabu kan matsayar kujerar gwamnan Bayelsa
Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri yayin taro a Yenagoa. Hoto: Douye Diri.
Source: Facebook

Matsayar lauyoyi kan kujerar Gwamna Diri

Amma Mallam Ahmed Raji (SAN) ya ce kundin tsarin mulki bai haramta hakan ba, domin an bukaci dan jam’iyya ne kawai a lokacin zabe.

Kara karanta wannan

Yaron Jonathan da ya taba zama 'dan majalisa ya watsar da PDP zuwa APC

Ya kara da cewa idan an kori mutum daga jam’iyyarsa, hakan ba yana nufin ya rasa kujerarsa ta siyasa kai tsaye ba, cewar ThisDay.

A cewar Abiodun Olatunji da Monday Ubani, kundin tsarin mulki ya fayyace lokutan da gwamna zai rasa mukaminsa kamar rasuwa, murabus, ko tsigewa.

Sun ce ficewa daga jam’iyya ba daya ba ne daga sauran wadannan dalilai, don haka Diri har yanzu yana da halaccin ci gaba da zama gwamna.

Norrison Quakers kuma ya ce lamarin ya nuna raunin tsarin jam’iyyun siyasa a Najeriya, inda akasarin ‘yan siyasa ke canza jam’iyya don morarsu ta kashin kai.

APC ta fara zawarcin gwamna Diri

Mun ba ku labarin cewa Tsohon dan majalisa Sunny-Goli ya bayyana cewa APC na fatan Gwamna Douye Diri zai koma cikinta bayan barin PDP.

Sunny-Goli ya ce ya kada kuri’a ga Diri duk da kasancewarsa dan APC saboda ya na da nagarta, kuma ya kawo ci gaba.

A makon jiya ne dai Diri ya fice daga PDP amma bai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai shiga ba tukuna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.