Yaron Jonathan da Ya Taba Zama ’Dan Majalisa Ya Watsar da PDP Zuwa APC
- Tsohon hadimin Goodluck Jonathan ya yi murabus daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya bayan ficewar gwamnan Bayelsa
- Dr. Waripamo-owei Dudafa ya fice daga PDP tare da komawa APC mai mulkin Najeriya domin ba da ta shi gudunmawa
- Ya ce rikice-rikicen PDP sun sa ya fice daga jam’iyyar inda ya bayyana cewa matsalolin cikin gida da rashin zaman lafiya na daga cikin dalilansa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yenagoa, Bayelsa - Kwana uku bayan ficewar gwamnan Bayelsa, Douye Diri daga PDP, jam'iyyar ta sake samun nakasu.
Tsohon hadimin Goodluck Jonathan, Dr. Waripamo-owei Dudafa, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da komawa APC.

Source: Facebook
Tsohon dan majalisar ya koma APC daga PDP
Rahoton Punch ya tabbatar da cewa Dudufa ya fice ne bisa zargin cewa jam’iyyar PDP ta gaza warware matsalolin cikin gida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na cikin wata wasika da ya aika wa shugaban PDP na Opokuma/Ayibabiri ta Kudu a ƙaramar hukumar Kolokuma Opukuma ta jihar Bayelsa.
Dudafa ya ce ya yanke shawarar barin jam’iyyar bayan yin dogon tunani tare da shawarar iyalansa da abokan siyasarsa.
Ya yaba da irin jajircewa da ya yi ga jam'iyyar lokacin da ya ke cikinta tare da tuno yadda ya yi aiki tare da masu gwazo.
Ya ce:
"Cikin rashin jin dadi nake miƙa takardar ficewata daga jam’iyyar PDP daga yau kuma nan take. A tsawon lokacin da na shafe ina cikin jam’iyyar, na kasance mai jajircewa wajen kiyaye manufofinmu da kimarmu na bai ɗaya, kuma ya kasance gata gare ni na yi aiki tare da mutane masu ƙwazo da sadaukarwa.”

Source: Original
Musabbabin Dudafa na barin PDP zuwa APC
Tsohon dan majalisar ya ce rikice-rikicen da ke damun PDP a matakin ƙasa sun gurgunta jam’iyyar, don haka ya ga dacewar komawa jam'iyyar APC.
Dan siyasar ya ce yana ganin APC tana samar da haɗin kai da damar gyara ƙalubalen da ke gaban jihar da ƙasa baki ɗaya domin inganta al'umma.
Ya kara da cewa:
"“Duk da cewa wannan shawara ta kasance mai wahala a gare ni, ina nan a shirye don ci gaba da bautawa muradun al’ummarmu, bisa ƙwarin gwiwar sadaukarwata wajen inganta jin daɗinsu da cigabansu.”
Dudafa ya gode wa PDP bisa damar da ta ba shi, amma ya ce yanzu lokaci ne na sabon shafi a siyasa don ci gaban al’umma, cewar Daily Post.
Sanatan PDP ya watsar da jam'iyyar zuwa APC
A wani labarin mai kama da wannan, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta sake samun koma baya a majalisar dattawa bayan ficewar daya daga cikin sanatocinta.
Sanata Benson Konbowei mai wakiltar Bayelsa ta Tsakiya ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Konbowei ya bayyana cewa babu wani dan siyasan da ya san abin da yake yi da zai ci gaba da zama har sai PDP ta warware rikicinta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

