2027: Gwamnan PDP a Enugu Ya Sauya Sheka, Ya Hade da Tinubu a APC

2027: Gwamnan PDP a Enugu Ya Sauya Sheka, Ya Hade da Tinubu a APC

  • Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC daga PDP a taron manema labarai da ya gudana a Enugu
  • Peter Mbah ya ce matakin ya biyo bayan dogon tunani ne domin neman hadin kai da gwamnatin tarayya wajen bunkasa jihar
  • Gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki zai ba Enugu da yankin Kudu maso Gabas damar samun karin tasiri a gwamnatin Bola Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gwamnan Jihar Enugu, Mista Peter Mbah, ya sanar da barinsa jam'iyyar PDP tare da shiga jam’iyyar APC.

Matakin ya kara rage wa 'yan adawa karfi a fagen siyasar Kudu maso Gabas, musamman ganin cewa PDP ce jam’iyyar da ke da dogon tarihi a yankin.

Gwamnan Enugu, Peter Mbah
Gwamna Peter Mbah yana wani jawabi. Hoto: Enugu State Government
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa a lokacin da yake jawabi a taron manema labarai a ranar Talata a birnin Enugu, Mbah ya bayyana dalilin sauya shekar.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: An ji dalilin da ya sa gwamnan PDP ya sauya sheka zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Mbah ya yi nazari kafin shiga APC

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya ce manufarsa ita ce tabbatar da sauyi mai ma’ana ga jama’ar jihar.

Ya bayyana cewa ya dauki lokaci mai tsawo yana nazari kafin yanke wannan shawara, wanda ya bayyana a matsayin:

“Mataki na hadin gwiwa domin gina jama’ar Enugu da Najeriya baki daya.”

Dalilin sauya shekar Gwamna Mbah

Gwamna Mbah ya ce shawarar ta samo asali ne daga burinsa na yin aiki da shugabannin da ke da hangen nesa irin na Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Peter Mbah ya ce yana ganin shugaba Tinubu a matsayin abokin tafiya mai hangen nesa da jarumtaka wajen yanke shawarar da za ta tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

Ya ce sauyin ba abu ne da aka dauka da wasa ba, domin dukkan manyan jami’an gwamnati, ‘yan majalisar jiha da ta tarayya, shugabannin kananan hukumomi sun amince.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi artabu da 'yan ta'adda ana batun sulhu a Katsina, mutum 12 sun kwanta dama

Martaninsa ga PDP kan sauya shekar

A cikin jawabin nasa, Mbah ya gode wa jam’iyyar PDP bisa goyon bayan da ta ba shi tun daga lokacin yakin neman zabe har zuwa nasararsa.

Sai dai ya nuna damuwarsa kan yadda muryar yankin Kudu maso Gabas ke yawan yin kasa a cikin jam’iyyar.

The Cable ta rahoto ya ce:

“Mun tsaya tare da PDP shekaru da dama, amma akasari ba a sauraron muryar Kudu maso Gabas.
"Wannan ya sa muka yanke shawarar neman sabon hadin kai domin amfanin jama’ar mu.”

Gwamna Mbah ya bayyana cewa komawarsa zuwa APC za ta bude sabon babi na cigaba a jihar Enugu.

Ya ce yana fatan wannan hadin gwiwa da gwamnatin tarayya za ta taimaka wajen kawo sababbin ayyuka, da bunkasa tattalin arziki da kuma karfafa tsaro a jihar.

Shugaban APC, Farfesa Yilwatda.
Shugaban APC na kasa na wani jawabi. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

Martanin 'yan adawa kan zaben 2027

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan adawa sun fara magana kan sauya lokacin babban zabe da ake shirin yi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kusa a APC ya fadi illar da ficewar Farfesa Pantami za ta yi wa jam'iyyar

Majalisar dokokin Najeriya ce ta fara maganar sauya lokacin zaben 2027 zuwa 2026 saboda wasu dalilai ta ta bayyana.

Jam'iyyar PDP, NNPP da LP sun yi magana kan lamarin, kuma wasunsu sun bayyana ra'ayoyin da suka yi karo da juna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng