Tinubu: Kungiyoyin Arewa, Yarbawa Sun Fitar da Matsaya a kan Zaben 2027

Tinubu: Kungiyoyin Arewa, Yarbawa Sun Fitar da Matsaya a kan Zaben 2027

  • Kungiyoyin Arewa Think-Tank (ATT) da Afenifere sun bayyana matsayarsu a kan wanda ya dace ya mulki Najeriya bayan babban zaben 2027
  • Kungiyoyin ATT da ta ziyarci shugaban Afenifere na kasa, Pa Reuben Fasoranti, a Akure, Jihar Ondo, ta jaddada muhimmancin zaman lafiya a kasar nan
  • Sun jaddada cewa zaman lafiya da hadin kan Najeriya sun fi muhimmanci fiye da kabilanci ko jam’iyya, saboda haka, sun tanadi kuri'arsu a zabe mai zuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ondo – Kungiyar Arewa biyu a inuwar Think-Tank (ATT) da kungiyar Afenifere, manyan ta Kudu maso Yamma, sun bayyana wanda za su zaba.

Kungiyoyin sun yanke hukuncin bayar da cikakken goyon bayansu ga sake tsayawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu takara a 2027.

Kara karanta wannan

Kusa a APC ya fadi illar da ficewar Farfesa Pantami za ta yi wa jam'iyyar

Asiwaju Bola ya samu goyon bayan Arewa da Kudu
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Ajuri Ngelale
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Shugaban ATT, Muhammad Alhaji Yakubu, ya jagoranci tawagar daga Arewa zuwa gidan shugaban Afenifere na kasa, Pa Reuben Fasoranti, a Akure, Jihar Ondo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu: Kungiyoyin Arewa, Afenifere sun gana

The Nation ta wallafa cewa bayan ganawar sirri, Muhammad Alhaji Yakubu ya shaida wa manema labarai cewa Arewa ta riga ta kuduri aniyar marawa Tinubu baya.

Ya ce goyon bayan ya samo asali ne daga adalci da tsarin mulki na karba-karba, inda ya jaddada cewa Arewa ba ta magana biyu.

Muhammad Alhaji Yakubu ya ce:

“Ko da wani ɗan Arewa ya nuna sha’awa, mun riga mun yanke hukunci. Dole mulki ya ci gaba da kasancewa a Kudu har sai bayan 2031.”
Kungiyoyin Arewa da Kudu na son a sake zaben Tinubu
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya bayyana ziyarar a matsayin wata hanya ta ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a tsakanin yankuna.

Kungiyoyin biyu sun nuna cewa ci gaban Najeriya ya dogara ne da adalci da gaskiya a cikin tattaunawar kowa da kowa.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Kwamishinoni da manyan hadiman gwamna sun bar PDP sun koma APC

Sun jaddada cewa kalubalen da ƙasar ke fuskanta, kamar matsalar tsaro, durkushewar tattalin arziki da rabuwar kawuna, na buƙatar haɗin kai da kishin ƙasa.

Muhammad Alhaji Yakubu ya yaba wa Tinubu bisa jajircewarsa da sauye-sauyen tattalin arziki da a yanzu ake gani a kasar nan.

Ya kara da cewa:

"Arewa Think-Tank ta zo ne don tabbatar wa Kudu maso Yamma da goyon bayan Arewa har zuwa 2031.”

Afenifere ta yabi Shugaba Tinubu

A jawabin Oba Olu Falae, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, wanda ya wakilci Pa Fasoranti, ya yaba da Tinubu bisa cire tallafin fetur da daidaita farashin canji.

Ya ce:

“Kwanon awon garri ya koma ₦700 daga ₦1,500, buhun garin rogo daga ₦450,000 ya koma ₦150,000. Wannan ci gaba ne sosai."

Apagun Kole Omololu, Sakataren Ƙungiyar Afenifere na Ƙasa, ya bayyana Tinubu a matsayin shugaban da ke da hangen nesa, jarumta da kishi.

Tinubu ya fusata 'yan uwan Bilyaminu

A baya, kun ji cewa 'yan uwan marigayi Bilyaminu Bello sun fitar da sanarwa inda suka bayyana cewa yafewa da Maryam Sanda da Shugaba Bola Tinubu ya yi abin takaici ne.

Kara karanta wannan

Jagora a APC ya fadi makomar Tinubu, Dikko Radda a zaben 2027

Sun ce wannan matakin ya sake dawo masu da ciwon rasa dan uwansu da aka kashe, kuma an ci mutuncin kotunan da suka yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya.

'Yan uwan Bilyaminu sun ce Maryam ba ta taɓa nuna nadama ba tun bayan kisan kuma yafe mata da aka yi wata hanyar sauƙaƙawa wa mai laifi ne da kuntata masu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng