Gwamna Bala Ya Fadi Abin da Yake Ji kan Gwamnonin da Ke Ficewa daga PDP zuwa APC
- Waau manyan jiga-jigai da suka hada har da gwamnoni sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC
- Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya nuna damuwarsa hakan
- Gwamna Bala ya nuna cewa bai isa ya hanasu yin hakan ba, don suna da 'yancin yin abin da suke so
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi magana kan masu ficewa daga jam'iyyar.
Gwamna Bala ya bayyana cewa gwamnonin da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC suna fuskantar kalubale a harkokin siyasa tun bayan barin jam’iyyar.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Asabar, yayin kaddamar da kwamitin sadarwa na babban taron jam’iyyar PDP.
Gwamna Bala Mohammed ya ce gwamnonin PDP suna aiki a hankali don haɗa kan jam’iyyar tare da tabbatar da karfinta yayin da ake shirin babban zaɓen 2027.
Wasu gwamnonin PDP sun koma APC
A baya-bayan nan, wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheƙa zuwa APC, ciki har da Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori; da kuma tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023, Ifeanyi Okowa.
Hakazalika wasu rahotanni sun nuna cewa gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya shirya komawa jam'iyyar APC.
Me Gwamna Bala ya ce kan masu komawa APC
Da yake mayar da martani kan hakan, Gwamna Bala Mohammed ya nuna damuwarsa kan yawaitar sauya sheka daga PDP zuwa APC.
"Idan aka tambaye ni ko ina cikin damuwa da irin yadda wasu gwamnoninmu ke sauya sheka zuwa APC, tabbas ina cikin damuwa sosai. Amma shugabanci nauyi ne."
"A matsayina na jagora a tsakanin takwarorina, ba zan iya hana su yanke shawara ba, amma muna yin aiki sosai a bayan fage don daidaita al’amura."
- Gwamna Bala Mohammed
Ya ce da ba don irin kokarin da ake yi ba, da sauya shekar da ake yi ta fi haka muni, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da labarin.
Gwamna Bala ya nuna yatsa ga gwamnatin APC
Gwamnan ya kuma yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta APC na gudanar da mulki ne da salo na neman mayar da kasar nan karkashin jam’iyya ɗaya.

Source: Twitter
"Ba zan ce takwarorina sun yi kuskure ba, suna da ‘yancin yin abin da suke so. Amma ina ta ba su shawara cewa ma fi yawansu da suka bar jam’iyyar ba sa samun saukin siyasa, domin mafi yawan talakawa a kasa ‘yan PDP ne kuma ba su farin ciki da sauya shekar.”
- Gwamna Bala Mohammed
Sanata Dahuwa ya yi murabus daga PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar Bauchi ta Arewa a majalisar dattawa, Samaila Dahuwa Kaila, ya yi murabus daga jam'iyyar PDP.
Sanatan ya bayyana cewa ya dauki matakin yin hakan ne saboda rikice-rikicen da suka addabi jam'iyyar.
Ya nuna cewa rikice-rikicen na PDP suna hana shi gudanar da aikin na wakilci yadda ya kamata a majalisar dattawa.

Kara karanta wannan
Gwamnoni 3 na shirin shiga APC, Gwamna Bala ya yi magana kan masu ficewa daga PDP
Asali: Legit.ng

