Abin da Tinubu Ya Ce ga ’Yan PDP, ADC Fiye da 60,000 da Suka Koma APC a Jigawa

Abin da Tinubu Ya Ce ga ’Yan PDP, ADC Fiye da 60,000 da Suka Koma APC a Jigawa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi mambobin jam'iyyun adawa da suka koma jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa
  • Tinubu ya karbi sama da yan adawa 60,000 daga jam’iyyun PDP da ADC da wasu a jihar wadanda suka gaji da zama a adawa
  • Shugaban ya tabbatar da cewa gwamnati za ta kammala hanyar Kano zuwa Maiduguri don bunƙasa tattalin arziki da sauƙaƙa sufuri

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutse, Jigawa - Shugaba Bola Tinubu, gwamnonin APC da jiga-jigan jam'iyyar sun cika a Jigawa domin karbar sababbin tuba daga jam'iyyun adwa.

Shugaba Tinubu ya karbi mutane 64,000 daga jam'iyyun adawa daga jihar Jigawa wadanda suka koma jam'iyyar APC mai mulki.

Tinubu ya karbi dubban yan adawa zuwa APC a Jigawa
Dandazon yan Jigawa da suka koma APC a Jigawa da Gwamna Buni da takwaransa, Umar Namadi. Hoto: @uanamadi.
Source: Twitter

Tinubu ya karbi dubban mutane zuwa APC

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Gwamna Mai Mala Buni wanda ya wakilci Bola Tinubu ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 3 na shirin shiga APC, Gwamna Bala ya yi magana kan masu ficewa daga PDP

A cikin sanarwar, Mamman Mohammed ya ce Tinubu ya yi alkawari ga sababbin tuban zuwa APC da cewa dukansu sun zama daya da tsofaffin yan jam'iyyar.

Shugaban ƙasar, wanda gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni (CON, COMN) ya wakilta, ya tabbatar wa sababbin mambobin cewa za a ba su kulawa da dama iri ɗaya da tsofaffin mambobin jam’iyyar.

“Daga yau za a rika kallonku daidai da tsofaffin mambobin jam’iyya, kuma muna alfahari da ƙarfin guiwar da kuka nuna wajen goyon bayan jam’iyya mai mulki da kudurinta na ci gaban ƙasa."

- Bola Tinubu.

Dubban yan adawa sun koma APC a Jigawa, Tinubu ya karbe su
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Alkawuran da Tinubu ya yi ga yan kasa

Shugaba Tinubu ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa wajen inganta tsaro a sassan ƙasa domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa da kuma farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta tabbatar da kammala hanyar Kano zuwa Maiduguri domin sauƙaƙa jigilar kayayyaki da samar da ci gaban tattalin arziki a yankin arewa.

Kara karanta wannan

Akpabio ya yi wa jam'iyyun adawa shagube a zauren majalisa

Ya kara da cewa:

“Gwamnati za ta tabbatar da kammala aikin hanyar Kano zuwa Maiduguri domin inganta zirga-zirga da bunƙasa tattalin arziki.”

Tinubu ya yabawa Gwamna Umar Namadi Danmodi bisa irin aikace-aikacen ci gaba da yake aiwatarwa a Jigawa, yana mai cewa hakan ya inganta rayuwar jama’a sosai.

A nasa jawabin, hadimin Tinubu kan harkokin siyasa, Kabiru Ibrahim Masari, ya roƙi al’ummar Jigawa su ci gaba da goyon bayan APC, ya tabbatar da cewa jihar za ta ci gaba da amfana daga gwamnatin tarayya.

“Ku goyi bayan jam’iyya, ina tabbatar muku Jigawa za ta ci gaba da amfana daga gwamnati mai ci."

- Cewar Masari

Tun da farko, Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa tallafi da haɗin kai daga gwamnatin tarayya ya taimaka wajen inganta rayuwar jama’ar Jigawa.

Gwamna Namadi ya yabawa mulkin Tinubu

Kun ji cewa ana ci gaba da bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan tazarcen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a zaben 2027 duk da bai ce zai yi takara ba.

Kara karanta wannan

Lambar Abba Kabir ta fito, malamin addini ya jero gwamnoni 4 da ka iya komawa APC

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba kan salon mulkin da Shugaba Tinubu yake yi a Najeriya.

Ya nuna cewa za su yi bakin kokari domin ganin cewa shugaban kasan ya sake komawa kan madafun iko a karo na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.