PDP za Ta Rushe: Gwamna, 'Yan Majalisa 24 da Kansiloli 260 za Su Koma APC
- Jam’iyyar PDP na shirin rushewa a jihar Enugu yayin da Gwamna Peter Mbah ke shirin jagorantar manyan ‘yan siyasa zuwa jam’iyyar APC
- Shugaban rikon kwarya na APC a jihar, Ben Nwoye, ya tabbatar da cewa Mbah da dukkan shugabannin PDP za su sauya sheka
- An ce sauyin siyasar zai kawo ƙarshen mulkin PDP na shekaru 25 a Enugu tare da ƙarfafa matsayin APC a yankin Kudu maso Gabashin kasar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Enugu - Jam’iyyar PDP ta shiga wani yanayi na rikicewa a jihar Enugu bayan sanarwar da ta nuna cewa Gwamna Peter Mbah zai jagoranci 'yan siyasar jihar zuwa APC.
Wannan mataki, kamar yadda manyan ‘yan siyasa suka bayyana, shi ne ƙarshen tasirin PDP a jihar.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa shugaban rikon kwarya na APC a Enugu, Dr Ben Nwoye ne ya bayyana hakan a babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Gwamna Mbah zai koma jam’iyyar APC tare da mambobin majalisun jiha da na ƙasa 24, kansiloli 260, da kuma dukkan shugabannin PDP na jihar.
APC vs PDP: Sauyin siyasar jihar Enugu
Dr Ben Nwoye ya ce sauya shekar mataki ne da zai sauya siyasar yankin Kudu maso Gabas gaba ɗaya, inda ya bayyana shi da “babban canji da zai kawo sabuwar dama ga yankin.”
A cewarsa:
“Ba gwamna kaɗai ne zai koma APC ba, yana tafe ne da dukkan 'yan PDP a jihar Enugu."
An bayyana sauyin da ake shirin yi a matsayin mafi girma a tarihin siyasar yankin tun 1999, domin zai kawo ƙarshen rinjayen PDP a jihar Enugu da ma yankin gaba ɗaya.
Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki zai buɗe ƙofofi ga APC wajen samun rinjaye a sauran jihohin Kudu maso Gabas kamar Anambra da Abia.
Jawabin shugabannin jam’iyyar APC
Shugaban APC, Farfesa Nentawe Yilwatda da ya kaddamar da kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar a Enugu, ya yaba da matakin gwamna Mbah, yana mai cewa APC gida ne ga kowa.
“Wanda ya zo jiya ko yau ko gobe, daidai ya ke da kowa. Manufarmu ita ce mu bunƙasa, mu lashe zaɓe, mu kawo nasara a 2027,”
- In ji shi.
Haka nan mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Emma Eneukwu, ya bayyana cewa wannan sauyi ya dawo da martabar yankin Kudu maso Gabas a siyasar ƙasa.

Source: Twitter
The Nation ta wallafa cewa ya ce:
“Ba za mu ƙara zama a baya ba. Da Enugu ta shiga APC, yankin Kudu maso Gabas ya dawo da muryarsa mai karfi a siyasa.”
An rusa shugabannin APC a Enugu
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta rusa shugabancinta a jihar Enugu yayin da ake jiran sauya shekar gwamnan jihar.
Bayan rusa shugabannin, APC ta nada Ben Nwoye a matsayin shugaban rikon kwarya da zai jagoranci jam'iyyar.
Rahotanni sun bayyana cewa shugabannin da aka kora na da kyakkyawar fahimta da ministan kimiyya da ya yi murabus.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


