'Shekara 4 kawai Zan Yi kan Mulki,' Dan Takarar Gwamnan ADC Ya Yi Rantsuwa a Kotu

'Shekara 4 kawai Zan Yi kan Mulki,' Dan Takarar Gwamnan ADC Ya Yi Rantsuwa a Kotu

  • Dan takarar ADC, John Nwosu, ya rantse a gaban kotu cewa idan ya ci zabe, zai yi wa’adi ɗaya ne kacal domin tabbatar da adalci
  • A cewar dan takarar, matakinsa zai tabbatar da kiyaye tsarin karba-karbar mulki tsakanin shiyyoyin siyasa uku na Anambra
  • Nwosu ya ba al'ummar Anambra tabbacin cewa shekaru hudu kacal sun ishe shi ya kawo muhimman sauye sauye a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC, Mista John Nwosu, ya rantse a gaban kotun koli da ke Awka kan zaben jihar na 2025.

Mista John Nwosu ya rantse cewa zai yi wa'adi daya ne kacal idan ya lashe lashe zaben gwamnan Anambra da za a gudanar a ranar 8 ga Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Zaben Ekiti: Gwamna ya tsallake da APC ta hana manyan 'yan siyasa 2 shiga takara

Dan takarar gwamnan Anambra na ADC ya yi rantsuwar yin wa'adi daya kacal idan ya ci zabe
Hoton dan takarar gwamnan Anmabra na ADC, John Nwosu, da ƴan kwamitin yakin neman zabensa a Awka. Hoto: @JohnCNwosu
Source: Twitter

A cewar rahoton jaridar Vanguard, Mista Nwosu na son ya tabbatar da adalci da kiyaye tsarin mulkin karba-karba shiyyoyin siyasar jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan takarar ADC zai mutunta tsarin karba-karba

A takardar rantsuwar da ya sanya wa hannu, Nwosu ya bayyana cewa yana da cikakken masaniya kan tsarin mulkin karba-karba tsakanin mazabu uku na Anambra.

Ya ce yana sane da cewa an kawo tsarin ne domin yin adalci, kawo daidaito da kuma kyakkyawan tafiyar da mulki a Anambra ta Arewa, Tsakiya da Kudu.

Dan takarar ya ce saura shekara hudu ga yankin Anambra ta Kudu, wanda ke kan mulki yanzu, ya miƙa mulki ga Anambra ta Tsakiya, inda shiyyar za ta yi mulki na tsawon shekaru takwas, kafin daga bisani a koma Anambra ta Arewa.

Ya kara da cewa bin wannan tsarin zai taimaka wajen kawar da sabani da rashin jituwa a tsakanin al’umma da ‘yan siyasa.

“Shekaru 4 sun isa sauya Anambra” - Nwosu

Kara karanta wannan

Manyan APC sun kori shugabannin jam'iyya, an nada masu rikon kwarya a Enugu

Da yake jawabi bayan sanya hannu a takardar rantsuwar, Nwosu ya bayyana cewa burinsa shi ne ya yi hidima ga jama’a, ba wai ya riƙe mulki don kansa ba.

“Na shiga takarar ne domin in yi wa al’umma hidima ba don wani muradin kai na ba. Na tabbatar da hakan a gaban kotu domin in nuna gaskiya ta."

- Mista John Nwosu.

Ya ƙara da cewa shekaru huɗu sun isa domin ya sauya fasalin Anambra, domin yana fatan gwamnatinsa za ta kasance mai riko da gaskiya da hangen nesa, inji rahoton Arise News.

Nwosu, wanda shi ma dan Anambra ta Kudu ne kamar gwamna mai ci, Farfesa Chukwuma Soludo, na daga cikin ’yan takara 16 da ke za su fafata a zaben gwamnan jihar.

Dan takarar gwamnan Anambra na ADC ya yi rantsuwar yin wa'adi daya kacal idan ya ci zabe
Taswirar jihar Anambra da ke a shiyyar Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An yabawa dan takarar gwamnan ADC

Anambra ta kasance tana amfani da wannan tsari na karba-karba, duk da cewa babu shi a dokance, don tabbatar da cewa kujerar gwamna tana zagayawa tsakanin shiyyoyi uku.

Da yake tabbatar da cewa zai yi wa’adi ɗaya kacal, wasu 'yan jihar sun bayyana cewa wannan mataki na Nwosu ya nuna tsantsar gaskiya, amana, da kishin al’ummarsa.

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021

Wasu sun nemi 'yan siyasa da su yi koyi da Nwosu, wajen mayar da hankali kan hidimatawa jama’a maimakon dadewa a kan kujerar mulki ba tare da aikin komai ba.

'Yan takara sun san ranar zaben Anambra

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jukumar INEC ta ce za ta gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra a ranar Asabar 8 ga watan Nuwamba, 2025

Shugaban hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa, ya bayyana hakan a Abuja a taron tuntubar juna da jam’iyyun siyasar da za su fafata a zaben gwamnan jihar.

INEC ta bayyana cewa jam'iyyun siyasa za su gudanar da zaben fitar da gwani daga 20 ga Maris 2025 zuwa 10 ga Afrilu 2025, domin tunkarar zaben gwamnan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com