Manyan APC Sun Kori Shugabannin Jam'iyya, an Nada Masu Rikon Kwarya a Enugu

Manyan APC Sun Kori Shugabannin Jam'iyya, an Nada Masu Rikon Kwarya a Enugu

  • Jam’iyyar APC ta rusa kwamitin shugabancin jihar Enugu tare da nada sabon kwamiti mai mambobi bakwai domin rikon kwarya
  • An sanar da rusa shugabancin ne bayan taron kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar karo na 179 a Abuja, karkashin Nentawe Yilwatda
  • Barista Ben Nwoye ya zama sabon shugaban rikon kwarya yayin da tsohon shugaban majalisar Enugu, Eugene Odo, ya zama sakatare

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta sanar da rushe shugabancin jam’iyyar a jihar Enugu tare da kafa sabon kwamitin rikon kwarya mai mambobi bakwai domin kula da harkokin jam’iyyar.

An yanke wannan hukuncin ne a ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025, yayin taron kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar karo na 179 a Abuja.

Shugabannin APC a Abuja
Shugaban APC da wasu 'yan jam'iyyar a ofis a Abuja. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

Legit ta tattaro bayanai kan matakin da APC ta dauka ne a wani sako da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na X.

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataki ya biyo bayan jita-jitar cewa ana shirin ganin Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya koma jam’iyyar APC.

An rusa shugabannin APC na jihar Enugu

Bayanin da ya fito daga taron ya nuna cewa kwamitin gudanarwa na kasa ya yanke shawarar rusa shugabancin jam’iyyar a Enugu karkashin Ugo Agballah.

Rahoton Daily Post ya nuna cewa an rusa shugabancin ne bayan nazarin da aka gudanar kan halin da jam’iyyar ke ciki a jihar.

Rusa shugabancin na zuwa ne bayan Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji ya yi murabus daga mukaminsa kwana biyu da suka gabata kan zargin takardun bogi.

Wani rahoto ya nuna cewa Uche Nnaji ya kasance abokin siyasa ne ga tsohon shugaban jam’iyyar a jihar.

APC ta nada kwamitin rikon kwarya

Kwamitin rikon kwarya da aka kafa zai fara aiki nan take, kuma za a kaddamar da shi a ranar Juma’a, 10 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 10:00 na safe, a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Rigiji gabji: Atiku ya nemi a binciki Tinubu da ministocinsa kan takardun bogi

Kwamitin yana karkashin jagorancin tsohon shugaban jam’iyyar a jihar, Ben Nwoye, yayin da tsohon shugaban majalisar dokokin jihar, Rt. Hon. Eugene Odo, zai rike mukamin sakatare.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Fidelia Njoeze, Peter Chime, Dr Oby Ajih, Dr Chiedozie Nwafor, da Emma Ekeh.

Shugaban APC na kasa, Farfesa Yilwatda.
Shugaban APC, Farfesa Yilwatda a wata ziyara da ya kai Filato. Hoto: All Progressive Congress
Source: Twitter

An bayyana cewa kwamitin zai gudanar da harkokin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zabe na shugabanni a jihar.

Karin bayani daga jam'iyyar APC

Sanarwar da ta fito daga ofishin mataimakin sakataren yada labaran APC, Hon. Durosinmi Meseko ta tabbatar da daukar matakin.

Ta bayyana cewa hukuncin ya samu amincewar shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda.

Shugaban APC ya cigaba da zama minista

A wani rahoton, kun ji cewa har yanzu shugaban APC na kasa Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda na cigaba da zama minista.

Rahotanni sun nuna cewa tun a watan Yulin 2025 Farfesa Nentawe Yilwatda ya maye gurbin Abdullahi Ganduje a shugabancin APC.

Sai dai tun bayan lokacin aka fara zuba ido domin ganin wanda zai maye gurbinsa a ministan jin kai amma har yanzu ba a nada wani ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng