Sanata Barau Ya Tabo Batun Tazarcen Tinubu, Ya Hango Abin da Mutanen Kano Za Su Yi a 2027

Sanata Barau Ya Tabo Batun Tazarcen Tinubu, Ya Hango Abin da Mutanen Kano Za Su Yi a 2027

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Sanata Barau ya nuna cewa shugaban kasan yana share musu hawayensu a duk lokacin da suka nemi wani abu a wajensa
  • Ya bayyana cewa zaben shekarar 2027, zai zama lokacin da za a rama biki kan alherin da Tinubu ke yi wa mutanen Kano da Arewa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Sanata Barau ya ce jam’iyyar APC, tare da mutanen Kano da yankin Arewacin Najeriya, za su sakawa Shugaba Tinubu alherin da yake musu a zaben shekarar 2027.

Sanata Barau ya yabawa Shugaba Bola Tinubu
Sanata Barau Jibrin tare da shugaban kasa Bola Tinubu. Hoto: @barauijibrin, @DOlusegun
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce Sanata Barau ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin kaddamar da shirin tallafin karatu ga ɗaliban jami’a a sabuwar jami’ar ilmi ta tarayya ta Yusuf Maitama Sule, Kano.

Kara karanta wannan

Sanata Barau zai raba tallafin N20,000 ga talakawa a Kano, an ji adadin da za su samu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Bola Tinubu ya samu yabo

A wajen taron, karamin ministan gidaje da raya birane, Yusuf Ata, shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, shugaban Jami’ar, Farfesa Abdullahi Kadage, da shugaban ASUU na jami’ar, Ado Abdullahi, duk sun yaba da irin kokarin Shugaba Tinubu.

“Ina son na gode wa shugaban kasa, wanda dukkanmu muna alfahari da shi, shugaba mai son Kano, mai son Arewa da Najeriya gaba ɗaya."
"Ya amince da rokonmu na shekaru da dama domin ɗaga darajar wannan makaranta zuwa jami’a, kuma muna matuƙar godiya.”

- Sanata Barau Jibrin

Barau ya ce za a zabi Tinubu a 2027

Ya bayyana cewa kokarin kafa jami’ar ya ɗauki kusan shekaru 10, kuma amincewar Shugaba Tinubu cikin gaggawa ta nuna cewa gwamnatinsa na da kwarin gwiwar bunƙasa ilmi, rahoton Daily Trust ya tabbatar da labarin.

“Ruwan da ya jika ka shi ne ruwa. Ba mu taɓa rokon shugaban kasa wani abu ba, ya ce ba zai yi ba. To me zai hana mu kaunace shi? Dole mu saka masa da alheri, kuma muna jiran lokacin yin hakan a 2027.”

Kara karanta wannan

Hankali ya kwanta: Babban alkawari da Tinubu ya yi ga Kiristocin Arewacin Najeriya

- Sanata Barau Jibrin

Sanatan ya kuma godewa Shugaba Tinubu saboda amincewa da sake sunan makarantar zuwa Yusuf Maitama Sule, domin girmama tsohon ɗan siyasa, jakada, kuma dattijon Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule.

“Na ji raɗaɗi lokacin da gwamnatin Kano ta yanzu ta soke sunan da tsohuwar gwamnatin Ganduje ta saka a wata cibiyar karatu don girmama Alhaji Maitama Sule."
"Lokacin da na gabatar da bukata ga Shugaba Tinubu na a saka sunansa a wannan jami’a, nan da nan ya amince. Wannan alama ce ta kaunar da yake nunawa Kano da jarumanmu."

- Sanata Barau Jibrin

Barau ya kaddamar da tallafin karatu a Kano
Sanata Barau Jibrin na jawabi a wajen bada tallafin karatu. Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter

Sanata Barau, wanda ya bayyana kansa a matsayin “uban jami’ar,” yayin da ya kira Shugaba Tinubu “kakan jami’ar,” ya kuma yi alkawarin tallafawa ci gaban jami'ar.

Ya kuma sanar da bayar da tallafin karatu ga ɗalibai 1,000 daga mazabar Kano ta Arewa, tare da alkawarin faɗaɗa shirin zuwa sauran yankunan jihar.

Barau zai raba tallafi a Kano

Kara karanta wannan

Babu boye boye, an ji dalilin da ya sa Bola Tinubu bai jawo matarsa ta karbi musulunci ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin zai raba tallafin kudi a Kano.

Sanata Barau zai raba tallafin ne na N20,000 ga mutum 10,000 marasa galihu a dukkanin kananan hukumomin Kano.

Za a gudanar da rabon tallafin ne bayan an kammala zabar mutanen da za su amfana da shirin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng