"Ka Saurari Matarka": Kusa a APC Ya ba Jonathan Shawara kan Takara da Tinubu a 2027

"Ka Saurari Matarka": Kusa a APC Ya ba Jonathan Shawara kan Takara da Tinubu a 2027

  • Tsohon dan takarar gwamnan jihar Legas, Abdul-Azeez Adeniran, ya ja kunnen tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan
  • Abdul-Azeez Adeniran ya bukaci Jonathan da kada ya yi kuskuren yin takara da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027
  • Kusan na jam'iyyar APC mai mulki ya bayyna cewa babu wani dan siyasa da zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Jagoran Lagos4Lagos Movement kuma kusa a jam'iyyar APC, Dr. Abdul-Azeez Adediran (wanda aka fi sani da Jandor), ya ba tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, shawara.

Abdul-Azaeez Adeniran ya gargadi Goodluck Jonathan da kada ya saurari masu cewa ya nemi takara a zaben 2027.

Jigo a APC ya ba Jonathan kan shawara a 2027
Shugaban kasa Goodluck Jonathan tare da Goodluck Jonathan. Hoto: @DOlusegun, @GEJonathan
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Jandor ya yi wannan bayanin ne yayin wata hira da aka yi da shi a ranar Lahadi, 5 ga watan Oktoban 2025 a Legas.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an ji dalilin da ya sa Atiku Abubakar ke jan kafa kan batun takara a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara kusa a APC ya ba Jonathan?

Ya ce tsohon shugaban kasan zai yi babban kuskure a siyasance idan ya tsaya takara, domin a cewarsa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai doke shi a zaɓen 2027.

“Ina bada shawara ga Jonathan da kada ya sake shiga takarar shugaban kasa. Wadanda ke ba shi shawara, yaudararsa suke yi."
"Tinubu gogaggen ɗan siyasa ne, wanda Jonathan ko wani ɗan siyasa ba za su iya kayar da shi a 2027 ba."
“Ban yarda da maganar cewa Jonathan ne kaɗai zai iya kalubalantar Tinubu ba. Tinubu shi ne mutum ɗaya da ya kayar da shi daga wajen gwamnati."
"Ba za ka iya kwatanta wanda ya samu kujera bayan ya sha wahala da wanda kawai ya farka da safe ne ya same ta a hannunsa ba."

- Abdul-Azeez Adeniran

Jandor wanda ya yi takarar gwamnan jihar Legas karkashin PDP a zaben 2023, ya ce Jonathan zai yi asarar lokacinsa idan ya kuskura ya tsaya takara a 2027, yana mai karfafa shi da ya ci gaba da hutunsa cikin mutunci.

Kara karanta wannan

Atiku ya shirya hakura da takara da Tinubu a 2027? An ji gaskiyar zance

"Ya kamata Jonathan ya saurari matarsa, Patience, wadda ta riga ta roke shi da kada ya sake tsayawa takarar shugaban kasa."

- Abdul-Azeez Adeniran

Jandor ya ba Jonathan shawara
Tsohon dan takarar gwamnan jihar Legas, Abdul-Azeez Adeniran. Hoto: @AbdulazeezAdeniran
Source: Twitter

Jandor ya yabawa Shugaba Bola Tinubu

A cewarsa, Tinubu mutum ne mai kwarewa da tasiri a siyasa, kuma duk wanda ya tsaya takara da shi yanzu zai fuskanci mummunan kaye, rahoton Daily Post ya tabbatar.

"Shugaba Tinubu ya yi abin a zo a gani wajen tafiyar da kasa. Ba makawa za a sake zaɓensa a 2027."

- Abdul-Azeez Adeniran

Jonathan ya aika sako ga 'yan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya taya 'yan Najeriya murnar cika shekara 65 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka.

Jonathan ya bukaci 'yan Najeriya da kada gwiwoyinsu su yi sanyi kan kalubalen da kasar nan take fuskanta ta fannoni daban-daban.

Tsohon shugaban kasan ya bukaci 'yan Najeriya da kada su karaya sannan su ci gaba da fatan ganin kasar nan ta kai inda ake so ta fuskar ci gaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng