Magana Ta Fito, An Ji Dalilin da Ya Sa Atiku Abubakar ke Jan Kafa kan Batun Takara a 2027

Magana Ta Fito, An Ji Dalilin da Ya Sa Atiku Abubakar ke Jan Kafa kan Batun Takara a 2027

  • Har yanzu dai babu tabbacin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar zai sake neman takara a 2027 ko zai hakura da neman mulki
  • Mai magana da yawunsa, Paul Ibe ya bayyana cewa Atiku na jan kafa wajen ayyana shirinsa na takara saboda ya maida hankali kan gina ADC
  • Wannan dai na zuwa ne bayan Atiku ya bayyana cewa a shirye yake ya marawa matashi baya idan ya kayar da shi a zaben fitar da gwani

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan ko tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai sake neman takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Sabanin wasu abokan gwagwarmayarsa a tsagin adawa, Wazirin Adamawa ya ci gaba da jan kafa, yana kaucewa fitowa karara ya bayyana shirinsa a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

"Ka saurari matarka": Kusa a APC ya ba Jonathan shawara kan takara da Tinubu a 2027

Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar.
Hoton tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar a wurin taro. Hoto: @Atiku
Source: Facebook

Daily Trust ta ce yayin da wasu manyan ’yan siyasa a jam’iyyar hadaka, ADC suka fito suka bayyana shirinsu na neman takara, har yanzu shiru ne daga bangaren Atiku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ɗan takarar LP, Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, na cikin wadanda suka shiga tseren neman takara a ADC, har sun yi alkawarin yin zango daya.

Atiku a shirye yake ya goyi bayan matashi

Sai dai ana cikin dakon Atiku, sai kuma ya bulla a wata hira da BBC Hausa yana cewa a shirye yake ya marawa matashi baya, lamarin da wasu suka fassara da cewa da yiwuwar ya hakura da takara.

Lokacin da aka tambaye shi kai tsaye ko zai tsaya takara a 2027, Atiku ya ce:

“Har yanzu lokaci bai yi ba tukuna. Idan lokacin ya yi zan yanke shawara kuma zan sanar da yan Najeriya. Abin da muke yi yanzu muna yin sa ne domin alheri ne ga ƙasa.”

Kara karanta wannan

Tikitin 2027: Cacar baki ta barke tsakanin magoya bayan Obi da Atiku a ADC

“Idan ɗan takara matashi ya kayar da ni a zaben fitar da gwani, zan amince da sakamakon, kuma na mara masa baya da zuciya ɗaya."

Me Atiku ke nufi da marawa matashi baya?

Sai dai bayan rahotannin sun bazu a kafafen sada zumunta da fassarar cewa Atiku ya yanke shawarar marawa matashi baya, ofishin yada labaransa ya fitar da karin haske.

Kakakin tsohon mataimakin shugaban kasa, Paul Ibe, ya ce an fassara hirar da aka yi da Atiku ba daidai ba.

"Mun yi nazari kan bidiyo da rubutaccen kwafin hirar kuma babu wurin da Atiku ya fito fili ya ce zai janye wa wani takara," in ji shi.

Paul Ibe ya jaddada cewa Atiku ya bayyana cewa matasa da sauran masu sha’awar takara za su iya fitowa su gwada sa'arsu, kuma idan matashi ya lashe zaben fitar da gwani, zai mutunta sakamakon ya kuma mara masa baya.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Hoton Atiku Abubakar a wurin kamfen din PDP. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Me yasa Atiku ke jan kafa kan batun takara?

A wata hira da aka yi da shi, Paul Ibe ya ƙara bayanin cewa Atiku ya ki sanar da shirinsa na takara ne saboda ya maida hankali kan gina dandalin siyasa mai karfi.

Kara karanta wannan

Siyasar Najeriya: Zuwa kotu da abubuwan da ake fada kan takarar Jonathan a 2027

Ya ƙara da cewa Atiku ya riga ya hade da hadakar ADC, inda yake halartar tarurruka tare da Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Masoyan Atiku na ganin zai sake neman takara a 2027 kuma zai samu nasara duba da yadda yan Najeriya suka shiga taitayinsu.

A wata gajeruwar hira ta wayar tarho da wakilin Legit Hausa, Kabiru Dogo, wani masoyin Atiku ya bayyana cewa wannan karon lokacin nasarar Wazirin Adamawa ne.

Ya ce mafi yawan yan Najeriya sun dawo daga rakiyar APC sakamakon wahalhalun da suka shiga bayan cire tallafin man fetur.

Kwamared Kabiru ya ce:

"Kamar yadda mai magana da yawunsa ya fada, na san Atiku zai yi takara kawai dai a jira lokaci, kuma ina ji a raina nasara ta mu ce. Ko babu kamfe, ba na tunanin yan Najeriya za su kara zabar APC."

ADC ta bukaci Atiku ya yi rijista

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta bukaci Atiku da sauran manyan siyasar da suka yi hadaka su gaggauta mallakar katin zama cikakken yan jam'iyya.

Kara karanta wannan

Atiku ya shirya hakura da takara da Tinubu a 2027? An ji gaskiyar zance

Jam’iyyar ta ce dole su je mazabunsu su yi rajista kafin ƙarshen shekarar nan ta 2025, in ba haka ba za su rasa matsayin zama mambobi.

Shugaban jam’iyyar ADC a jihar Adamawa, Shehu Yohanna, ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da aka yi da shi a Yola.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262