Za a Rataye Tsohon Gwamna kan Badakalar N1trn a Najeriya? Mun Samu Karin Bayani
- Wata sanarwa da ta yadu a kafofin sadarwa ta yi ikirarin cewa za a yanke wa tsohon gwamnan hukuncin kisa ta hanyar rataya
- Majiyar ta ce ana zargin tsohon gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu da badakalar N1trn wanda ya jawo yanke masa hukuncin
- Binciken kwa-kwaf ya nuna wannan labari ƙarya ne, babu wani alkalin kotu mai suna Chukwuemeka Nwogu da ya yanke hukuncin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umuahia, Abia – Wata sanarwa da ta karade shafukan sada zumunta ta yi ikirarin cewa za a yankewa tsohon gwamna hukuncin kisa.
Rahoton ya ce za a yankewa tsohon gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu hukuncin kisa ta hanyar rataya kan zargin karkatar da N1trn.

Source: Twitter
Binciken TheCable ya tabbatar da cewa labarin ba gaskiya ba ne babu inda wani alkali ya yanke wannan hukunci.
Tarihin tsohon gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu
An haife tsohon gwamnan Abia kuma fitaccen dan siyasa a ranar 18 ga Oktobar 1964, wanda ya mulki Jihar Abia.
Ikpeazu ya yi mulki daga 29 ga Mayun shekarar 2015 zuwa 29 ga Mayu 2023, an zaɓe shi a karkashin jam’iyyar PDP.
Ya tsaya takara a zaɓen majalisar dattawa na 2023 domin wakiltar Abia ta Kudu a majalisar amma ya zo na uku bayan Sanata Enyinnaya Abaribe na APGA.
Zargin da ake yi wa tsohon gwamnan
Wasu rahotannin bogi sun yi zargin cewa an gano kuɗin a asusunsa a kasar Australia, inda aka ce an ware kuɗin ne don filin jirgin sama da aikin dogo a Abia.
An kuma danganta hukuncin da wani alkalin kotu da aka kira Chukwuemeka Nwogu, wanda aka ce ya ce shaidar da aka gabatar masa ta isa har a yankewa Ikpeazu hukuncin kisa.
Sai dai binciken kwa-kwaf ya gano cewa dokar Najeriya ba yanke hukuncin kisa kan laifin cin hanci da rashawa, illa dai hukuncin dauri a gidan yari.

Kara karanta wannan
Gwamna Fintiri ya yi afuwa ga masu laifi don murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun 'yanci
Bincike a rukunin yanar gizon kotunan jihar Abia ya nuna babu wani alkalin da ake kira Chukwuemeka Nwogu a kujerar shari’a.

Source: Twitter
Binciken kwa-kwaf kan rahoton yanke hukuncin
Haka kuma babu wata jarida ta cikin gida ko ta kasashen waje da ta ruwaito irin wannan hukunci, wanda da ace gaskiya ne da ya mamaye kafafen yada labarai.
Tsohon kwamishinan kasuwanci a Abia, John Kalu ya bayyana cewa wannan labari bogi ne kawai, yana mai cewa Ikpeazu ba shi da wata shari’a da yake fuskanta a kowace kasa.
Binciken ya kammala da cewa wannan jita-jita ƙarya ce tsagwaronta, kuma ƙirƙirar alkalin da babu shi na nuni da cewa an kitsa labarin ne domin yaudara.
Gwamnan Abia ya bukaci N100bn kan bata suna
Mun ba ku labarin, gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya nuna damuwa kan yada wasu bayanai a manhajar Facebook da ke zubar masa da mutunci.
Alex Otti ya nemi diyya ta Naira biliyan 100 daga tsohon kwamishina, Eze Chikamnayo kan wallafe-wallafen bata suna.
Lauyan gwamnan ya ce rubuce-rubucen suna nufin nuna kiyayya da ɓata martabar Otti, wanda ya ce ba a taba tuhumarsa a kotu ba.
Asali: Legit.ng
