Babbar Magana: Atiku Ya Ce zai iya Hakura da Buga Takara da Tinubu a 2027
- Tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriya, Atiku Abubakar ya yi magana kan hakura da takara a zaben 2027 mai zuwa
- Ya bayyana cewa yanzu yana maida hankali ne kan gina sabuwar jam’iyyar hadaka ta ADC tare da ƙarfafa matasa da mata
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zargin cewa APC ta mamaye PDP, dalilin da ya sa ya fice daga jam’iyyar a Yulin 2025
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yi magana kan takarar 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa Atiku Abubakar ya yi magana kan yiwuwar hakura daga takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Source: Facebook
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi da BBC Hausa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku Abubakar zai iya hakura da takara
Atiku Abubakar ya ce zai iya hakura daga takarar shugaban ƙasa a 2027 idan matashi ya kayar da shi a zaben fitar da gwani.
Ya bayyana cewa zai ba matashin cikakken goyon baya tare da horar da shi a harkokin siyasa idan har ya yi nasarar samun tikitin jam’iyya.
Furucin Atiku ya janyo magana a tsakanin masu sharhi, musamman ganin cewa yana daya daga cikin manyan ’yan siyasar da ake sa ran za su kara da shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Sauya sheka daga PDP zuwa ADC
A watan Yulin shekarar 2025, Atiku Abubakar ya fita daga jam’iyyar PDP, inda ya bayyana cewa jam’iyyar ta lalace saboda mamayar jam’iyyar APC mai mulki.
A cewarsa, hakan ya tilasta masa da wasu manyan ’yan adawa kafa sabuwar tafiyar hamayya a jam’iyyar ADC.
Ya ce wannan sabon matakin na siyasa ya ba shi damar ƙarfafa jam’iyya mai sauƙin karɓuwa ga matasa da mata, domin su samu dama wajen taka rawa a siyasar ƙasa.

Kara karanta wannan
"Sai an je gaban kotu," Fadar shugaban kasa ta kara tabo batun takarar Jonathan a 2027
Atiku ya jaddada cewa burinsu shi ne samar da sabuwar hanya da za ta ceto Najeriya daga matsalolin da take fuskanta.

Source: Facebook
Tarihin takarar Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya dade yana fafutukar neman zama shugaban ƙasa tun bayan barin kujerar mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007.
Ya nemi takara a 2023 a jam’iyyar PDP, daga baya ya koma jam’iyyar AC, wadda daga ƙarshe ta haɗu da wasu jam’iyyu ta kafa jam’iyyar APC.
Tun bayan barin ofis Atiku ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ’yan siyasar da ke da burin mulkin Najeriya.
Duk da haka, ya sha fuskantar ƙalubale a fagen siyasa, lamarin da bai taɓa hana shi ci gaba da fafutuka ba.
Jam'iyyar ADC ta bukaci Atiku ya yi rajista
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta bukaci masu hadaka a ADC su gaggauta tabbatar da cewa sun yi rajista.
Shugaban ADC a jihar Adamawa ya bukaci Atiku Abubakar da ya yi rajista domin samun damar zama cikakken dan jam'iyya.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan Atiku Abubakar, ADC a Adamawa ta bukaci Babachir Lawan da ya gaggauta rajista.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
