Fadar Shugaban Kasa Ta Kara Tabo Batun Takarar Jonathan a 2027, Ta Ce Zai Fuskanci Shari'a

Fadar Shugaban Kasa Ta Kara Tabo Batun Takarar Jonathan a 2027, Ta Ce Zai Fuskanci Shari'a

  • Fadar Shugaban Kasa ta ce Goodluck Jonathan na da ikon bayyana aniyarsa ta shiga takara a zaben 2027 mai zuwa
  • A karshen makon nan, jita-jitar cewa tsohon shugaban kasar zai dawo fagen siyasa kuma ya nemi takara ta kara karfi
  • Sai dai mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce kotu ce kadai za ta iya tantance halascin takarar Jonathan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa kotu ce kadai za ta iya tantance ko tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya cancanci tsayawa takara bisa tsarin doka ko a’a.

Mai Bai wa Shugaba Bola Tinubu Shawara na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan ranar Litinin.

Tsohon Shugaban Kasa, Dr. Goodluck Jonathan.
Hoton tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan a wurin taron PDP Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Daily Trust ta tattaro cewa Jonathan, wanda aka zabe shi tare da tsohon Shugaba Umar Musa ‘Yar’Adua a 2007, ya gaji kujerar mulki bayan rasuwar uban gidansa a ranar 5 ga Mayu, 2010.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta yi maraba da takarar Tsohon Shugaba Jonathan a 2027

Ya kammala ragowar wa’adin sannan ya kara samun cikakken wa’adi na shekaru 4 bayan lashe zaben 2011.

Sai dai a 2015, ya sake neman tazarce amma ya sha kaye a hannun tsohon Shugaban Kasa, Marigayi Muhammadu Buhari.

Ya halasta Jonathan ya nemi takara a doka?

A wata sanarwa da ya fitar da yammacin Litinin, Onanuga ya jaddada cewa Jonathan na da ‘yancin bayyana aniyarsa ta shiga takara idan yana so, amma kotu za ta yanke hukunci a kan batun.

“Shugaba Jonathan na da ‘yancin tsayawa takara idan yana so. Wannan hakki ne da ba za a iya kwace masa ba. Shugaba Tinubu zai yi maraba da shi idan ya yanke shawarar shiga takara. Amma Dole Jonathan ya fuskanci shari’a.
"Alƙalai ne za su tantance ko Jonathan, wanda aka rantsar sau biyu a shugabancin kasa, ya cika sharuddan kundin tsarin mulki da zai ba shi damar sake neman takara da kuma rantsar da shi idan ya yi nasara, a karo na uku."

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Rikici ya kunno kai tsakanin magoya bayan Peter Obi da jam’iyyar ADC

- Bayo Onanuga.

Onanuga ya soki gwamnatin Jonathan

Ya kuma sake tabo tarihin mulkin Jonathan, yana mai cewa gwamnatinsa ta bar tattalin arziki kasar nan cikin mummunan hali, Leadership ta rahoto.

“Ba za mu manta da gwamnatinsa cikin sauri haka ba, ba ta da tsayayyar manufa ta tattalin arziki, ta yi almubazzaranci, ta durkusar da tattalin arzikin kasa tare da jefa kasar cikin mawuyacin hali.
"Faduwar tattalin arzikin kasa, wanda Shugaba Tinubu ke aiki tukuru domin ya gyara, ta fara ne tun a lokacin mulkin Shugaba Jonathan,” in ji shi.
Bayo Onanuga.
Hoton mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shin Jonathan zai sake fitowa takara a 2027?

A wani labarin, kun ji cewa tsohon ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Farfesaa Jerry Gana ya yi ikirarin cewa Jonathan zai fito takara a 2027.

Jerry Gana ya ce Jonathan zai nemi kujerar shugaban kasa a 2027 karkashin iniwar jam'iyyar PDP, kuma yana da kwarin gwiwar zai kayar da Tinubu.

Kara karanta wannan

'Goodluck Jonathan zai yi takara kuma ya lashe zabe a shekarar 2027'

Tsohon Ministan ya ce ‘yan Najeriya sun gwada shugabanni biyu bayan Jonathan, kuma yanzu suna kaunar dawowarsa kan karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262