ADC Ta Gargadi Atiku Abubakar kan Rashin Mallakar Katin Zama Dan Jam'iyya

ADC Ta Gargadi Atiku Abubakar kan Rashin Mallakar Katin Zama Dan Jam'iyya

  • Shugaban jam’iyyar ADC a Adamawa ya ce dole manyan ‘yan siyasa su yi rijista a mazabunsu kafin karshen shekara
  • Ya gargadi Atiku Abubakar da Babachir Lawal cewa ba za su ci gaba da zama ‘yan jam’iyya ba tare da katin rijista ba
  • Shugaban ya yi gargadi da cewa duk wanda bai yi rajista ba, ba shi da hurumin rike mukami ko yanke shawara a ADC

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Adamawa – Jam’iyyar ADC ta fitar da sabuwar sanarwa ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal.

Jam’iyyar ta ce dole su je mazabunsu su yi rajista kafin ƙarshen shekarar nan, in ba haka ba za su rasa matsayin zama mambobi a bisa doka.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda na yi wa Kiristocin Najeriya kisan kiyashi? Minista ya tsage gaskiya

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: Paul O Ibe
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa shugaban jam’iyyar ADC a jihar Adamawa, Shehu Yohanna, ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da aka yi da shi a Yola.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an buɗe rijistar jam’iyyar kuma duk wanda bai mallaki katin zama mamba ba, ba za a amince da shi a matsayin ɗan jam’iyya ba.

Jam'iyyar ADC ta gargadi Atiku da Babachir

Yohanna ya ce babu wanda zai ci gaba da yanke shawara a madadin jam’iyya alhali ba shi da rijista.

Legit ta rahoto cewa ya bayyana cewa hakan saba wa kundin tsarin mulki ne, kuma yana rage darajar jam’iyyar a idon jama’a.

A cewarsa:

“Atiku Abubakar ya tafi mazabarsa ta Jada ya yi rajista, haka kuma Babachir ya tafi Hong ya yi rajista. Wannan shi ne kawai hanyar da za su kasance ‘yan jam’iyya na gaskiya.”

Ya kuma yi kira ga manyan ‘yan siyasa da suka haɗu a ADC daga jam’iyyu daban-daban su yi rajista domin tabbatar da cewa jam’iyyar ta samu nagartaccen tsari.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Peter Obi sun tanka bayan ADC ta ba'yan hadaka umarni

Yohanna ya tunatar da cewa sakataren yaɗa labarai na kasa na ADC, Bolaji Abdullahi, ya riga ya sanar da cewa dole ne mambobin haɗaka su fita daga tsofaffin jam’iyyunsu su yi rajista a ADC.

Atiku da makomar takararsa a ADC

Rahotanni sun bayyana cewa Atiku Abubakar yana nazari kan yiwuwar tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin ADC a 2027.

Sai dai duk da haka, an dakatar da shirin rajistarsa da aka sanar zai gudana a watan Agusta a Jada ba tare da wani bayani ba.

Atiku Abubakar da wasu 'yan ADC a Abuja
Atiku Abubakar da wasu 'yan ADC a Abuja. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

ADC ta shirya fafatawa a 2027

Yohanna ya nuna cewa APC da PDP ba su da karfin da za su iya kayar da ADC a babban zaɓe mai zuwa, inda ya ce manufofin gwamnatin APC sun bude kafa ga ADC domin ta karɓi mulki.

Haka kuma ya bayyana cewa jam’iyyar tana da fitattun ‘yan takara musamman a Adamawa, wadanda ya ce za su taka rawar gani.

Jonathan ya hadu da shugaban ADC

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya gana da shugaban jam'iyyar ADC, David Mark.

Jagororin sun gana ne a birnin tarayya Abuja bayan wani gagarumin taron ADC da ya hada jiga jigan jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Kazamin rikicin manoma ya firgita Darazo, ya hana zuwa gona a Bauchi

A lokacin da shugaba Goodluck Jonathan ke mulkin Najeriya, David Mark ne ya zama shugaban majalisar dattawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng