Komai na Iya Faruwa: Shugaban APC Ya Sanya Labule da Farfesa Pantami a Abuja

Komai na Iya Faruwa: Shugaban APC Ya Sanya Labule da Farfesa Pantami a Abuja

  • Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai ziyara gidan Farfesa Isa Ali Pantami a Abuja inda suka tattauna batutuwa da dama
  • Pantami ya bayyana cewa sun shafe shekaru tare a jami’a lokacin da Nentawe ke yin digiri na biyu, inda suka tuna lokutan farin ciki
  • A cewar Pantami, sun tattauna kan ilimi, tattalin arziki, mulki da kuma jana’izar mahaifiyarsa, yana mai godiya bisa wannan muhimmiyar ziyara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban jam'iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda na ci gaba da ziyarce-ziyarce domin farfado da ita.

Tun bayan hawansa shugabacin APC, Nentawe ya sha alwashin kawo sauyi da kuma tattaunawa domin kara kwace wasu jihohi.

Shugaban APC, Farfesa Nentawe ta kai ziyara ga Farfesa Pantami a Abuja
Shugaban APC a Najeriya, Nentawe Yilwatda, da Farfesa Isa Ali Pantami. Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda, Prof. Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Farfesa Isa Ali Pantami ya wallafa a shafinsa na X inda ya tabbatar da ganawa da Farfesa Nentawe a gidansa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Zargin taba annabi: Sheikh Bala Lau ya magantu kan rawar hukumar DSS a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mukaman da Pantami ya rike a siyasa

Pantami ya taba rike mukamin shugaban hukumar NITDA a zamanin mulkin Muhammadu Buhari wanda ya rasu a watan Yulin 2025.

Daga bisani, marigayi Buhari a nada shi a matsayin minista daga jihar Gombe wanda ya rike ma'aikatar sadarwa daga shekarar 2019 zuwa 2023.

Pantami ya gana da shugaban APC

A cikin bidiyon da ya wallafa, an gano lokacin da Pantami ya tarbi Nentawe inda ya yi masa iso da ba shi wurin zama.

Pantami ya tabbatar da cewa ya dade da sanin Nentawe tun a Jami'a lokacin da shugaban APC ke digiri dinsa na biyu.

Tsohon ministan ya ce sun tattauna batutuwa masu muhimmanci yayin zaman da ya yi da Nentawe wanda shi ma tsohon minista ne.

Farfesa Pantami ya karbi bakuncin shugaban APC
Tsohon minista, Farfesa Isa Ali Pantami a yayin taro a Abuja. Hoto: Prof. Isa Ali Pantami.
Source: Facebook

Batutuwan da tsofaffin ministocin suka tattauna

Daga cikin abubuwan da suka tattauna kamar yadda ya tabbatar akwai sha'anin mulki da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Ewugu: Tsohon mataimakin gwamnan da 'yan bindiga suka sace kafin ya rasu

Har ila yau, sun yi magana kan rasuwar mahaifiyarsa da ta rasu a kwanakin baya da batun ci gaban ilimi da sauran batutuwa masu muhimmanci.

A cikin rubutunsa, Farfesa Pantami ya ce:

"A daren jiya Asabar na samu ziyarar abota daga Mai Girma Farfesa Nentawe Yilwatda, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.
"Farfesa Nentawe da ni mun shafe wasu shekaru tare a jami’a lokacin da yake gudanar da karatun digirinsa na biyu a can.
"Mun tuna da kyawawan lokutanmu na jami’a cikin farin ciki. Haka kuma mun tattauna ilimi, tattalin arziki, mulki, da jana’izar mahaifiyarsa, da sauran batutuwa.
"Muna matukar godiya bisa wannan ziyara da shugaban jam’iyyar APC ya kawo mana."

Legit Hausa ta tattauna da masoyin Farfesa

Isa Umar Lastdon daga Gombe ya ce suna tare da Pantami a duk inda ya ke a siyasance.

Sai dai ya ce ya kiyayi mutanen APC saboda halin da suka jefa Najeriya na iya shafar siyasarsa.

Ya ce:

"Muna tare da Malam Isa Pantami kuma muna masa fatan samun mulkin jihar Gombe amma APC ba abin yarda ba ne saboda yanayin mulkin da suke yi."

Kara karanta wannan

Atiku ko Tinubu: Kawunan magoya bayan Buhari na CPC ya rabu a kan zaben 2027

Ya shawarci matasa da al'ummar jihar Gombe su marawa Malam baya domin samun nasara a zaɓen da ke tafe.

Atiku ya kai ziyara ta musamman ga Pantami

A baya, mun ba ku labarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, a gidansa da ke Abuja.

Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa masu muhimmanci kamar tattalin arziki, ilimi, da sauransu yayin da ake ta hasashe game da siyasa da zaben shekarar 2027.

Hakan na zuwa ne yayin da jama'iyyar ADC ta adawa ke kara karfi wanda ake hasashen Farfesa Pantami na shirin komawa cikinta bayan rike mukamin minista a gwamnatin APC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com