Shirin Kifar da Tinubu: Jonathan Ya Hadu da Shugaban Hadaka na Jam'iyyar ADC

Shirin Kifar da Tinubu: Jonathan Ya Hadu da Shugaban Hadaka na Jam'iyyar ADC

  • Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya kai ziyara ga shugaban ADC, Sanata David Mark, a daren Alhamis
  • Ziyarar ta biyo bayan taron farko na kwamitin koli na jam'iyyar hadaka ta ADC da aka gudanar a birnin tarayya Abuja
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da jin rade-radin yiwuwar Jonathan ya shiga takarar shugaban ƙasa a 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya kai ziyara ga shugaban jam’iyyar hadaka ta ADC, David Mark, a daren Alhamis.

Wannan ziyara ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rade-radin cewa Jonathan na iya shiga takarar shugaban ƙasa a 2027.

Jonathan yayin ganawa da shugaban jam'iyyar ADC
Jonathan yayin ganawa da shugaban jam'iyyar ADC. Hoto: ADC Vanguard
Source: Facebook

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa akwai alamar ziyarar na da alaka da mu'amala me kyau da ke tsakanin David Mark da Jonathan.

Kara karanta wannan

Ganduje ya fito da bayanai kan maganar sauya shekar Kwankwaso zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Goodluck Jonathan ya ziyarci shugaban ADC

Ziyarar Jonathan ga Mark ta biyo bayan taron farko na kwamitin koli na jam’iyyar ADC da aka gudanar a Abuja.

Wannan lamari ya ƙara hura wutar hasashen cewa tsohon shugaban na iya shiga hadakar ADC yayin da ake kira ya fito takara a gaba.

Wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar adawa sun riga sun fara zawarcin Jonathan don ya shiga takarar shugabancin ƙasa, inda ake so ya fuskanci, Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Alakar Jonathan da Sanata David Mark

Goodluck Jonathan ya riga ya yi wa Najeriya mulki kafin ya sha kaye a hannun marigayi Muhammadu Buhari a 2015.

Idan ya sake tsayawa, zai iya yin wa’adi guda kawai saboda kundin tsarin mulkin ƙasa bai yarda ya yi fiye da haka ba.

David Mark, wanda Jonathan ya kai wa ziyara, shi ne shugaban majalisar dattawa a lokacin mulkinsa.

Kara karanta wannan

ADC ko ADA: 'Yan hadaka sun kammala zabar jam'iyyar da za su yi takara a 2027

A wancan lokaci, dangantaka mai ƙarfi ta haɗa su, musamman lokacin da majalisar ta ba Jonathan damar zama shugaban rikon kwarya kan rashin lafiyar Umaru Musa Yar’Adua.

Shugaba Jonathan a lokacin da ya ke mulki
Shugaba Jonathan a lokacin da ya ke mulki. Hoto: Goodluck Ebele Jonathan
Source: Getty Images

Me Mark ya tattauna da Jonathan?

Ko da yake ba a bayyana ainihin manufar tattaunawar ba, masana harkokin siyasa na ganin cewa ziyarar ta ƙara jefa haske kan yiwuwar Jonathan na dawowa fagen siyasa gadan gadan.

Akwai masu ganin cewa ADC na iya zama sabon dandamali gare shi, musamman idan aka samu matsala a cikin PDP.

Jonathan ya yi wannan ziyara ne bayan dawowarsa daga Ghana, inda gidauniyarsa ta shirya wani taron dimokuradiyya.

Ya wallafa a X cewa:

“Mu haɗa hannu wajen kare dimokuradiyya domin ita ce hanya mafi inganci ta tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da ci gaba a nahiyar Afrika”

'Yan adawa za su hadu karkashin ADC

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar hadaka ta ADC ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a birnin tarayya Abuja.

Manyan 'yan siyasa da suka hada da Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa'i, David Mark da sauransu duk sun hallara taron.

Kara karanta wannan

Atiku ko Peter Obi: Kungiya ta fadi wanda ya kamata ya hakura da takara a 2027

A jawabin karshen taro da suka fitar, sun bayyana cewa sun amince da haduwa karkashin ADC domin tunkarar APC a 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng