ADC ko ADA: 'Yan Hadaka Sun Kammala Zabar Jam'iyyar da Za Su Yi Takara a 2025

ADC ko ADA: 'Yan Hadaka Sun Kammala Zabar Jam'iyyar da Za Su Yi Takara a 2025

  • Hadakar 'yan adawa ta cin ma matsaya kan jam'iyyar da za su yi amfani da ita a zaben shekarar 2027
  • 'Yan hadakar sun jingine batun sabuwar jam'iyyar ADA wadda hukumar INEC ba ta kammala yi wa rajista ba
  • Hakazalika, masu neman takarar shugaban kasa a ADC sun cimma matsaya kan wanda za su goyawa baya bayan zaben fidda gwani

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hadakar jam’iyyun adawa da ke neman kifar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu daga mulki a 2027, ta tsayar da ADC a matsayin jam'iyyar da za ta yi amfani da ita.

Hadakar 'yan adawan ta nesanta kanta daga sabuwar jam'iyyar siyasa da ba a gama yi wa rajista ba, wato ADA.

'Yan hadaka sun zabi jam'iyyar ADC
Hoton Atiku Abubakar da sauran 'yan hadaka a wajen taron ADC Hoto: @atiku
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce mai magana da yawun jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Shirin kifar da Tinubu: Jonathan ya hadu da shugaban hadaka na Jam'iyyar ADC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jiga-jigan hadaka sun gudanar da taro

A cewar Bolaji Abdullahi hakan na ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da shugabannin jam’iyyar suka cin ma a wani taro da suka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 25 ga watan Satumban 2025.

Jam’iyyar ADC ta kuma nemi mambobinta da ke cikin wasu jam’iyyu su yi murabus domin barin inda suke, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da labarin.

Daga cikinsu akwai Peter Obi na LP, Nasir El-Rufai na ADP, da kuma Sanata Aminu Tambuwal na PDP, domin su shigo cikin sabuwar tafiyar gaba dayansu.

Cikin waɗanda suka halarci taron akwai Shugaban jam’iyyar na kasa, David Mark, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; sakataren jam’iyyar na kasa, Rauf Aregbesola.

Sauran sun hada da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal da kuma tsohon gwamnan Rivers, Chibuike Amaechi.

Hadakar ta ta kuma sanar da kammala alakarta da ADA, inda Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Ganduje da jiga jigan APC a Kano sun cimma matsaya kan batun goyon bayan Tinubu

“Hadakar ta rufe duk wani al’amari da ya shafi ADA. Wannan na nufin ba su da sha’awar yin rajista ko rashin yin rajistar kungiyar.”
Hadaka ta zabi ADC don takara a 2027
Mai magana da yawun jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi @BolajiADC
Source: Facebook

'Yan hadaka sun cin ma matsaya kan 2027

Game da babban zaben shekarar 2027, Bolaji Abdullahi ya ce dukkan masu neman tikitin shugaban kasa a karkashin jam’iyyar sun amince za su goyi bayan wanda ya yi nasara a zaɓen fidda gwani.

"Dukkan ‘yan takarar shugaban kasa sun amince za su goyi bayan duk wanda ya lashe zaɓen fidda gwani."

- Bolaji Abdullahi

Ya kara da cewa kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) zai sanar da ranakun yin zaɓen fitar da gwani a jihohin Osun da Ekiti nan bada jimawa ba.

An bukaci Atiku ya hakura da takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar 'Save Democracy Mega Alliance' (SDMA), ta ba tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar, shawara kan zaben shekarar 2027.

Kungiyar ta bukaci da ya hakura da fitowa takarar shugaban a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Hakazalika, kungiyar ta bukaci Atiku kan ya marawa Peter Obi baya domin zama shugaban kasa a karkashin jam'iyyar ADC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng