Sule Lamido ya Ci Alwashin Hada Kan 'Yan Siyasar Najeriya, Ya Fadi Tsarinsa

Sule Lamido ya Ci Alwashin Hada Kan 'Yan Siyasar Najeriya, Ya Fadi Tsarinsa

  • Sule Lamido, tsohon gwamnan Jigawa, ya ce PDP za ta dage wajen haɗa kan manyan ‘yan siyasar ƙasar nan domin taimakon jama'a
  • Sule Lamido ya bayyana cewa haɗin gwiwar shugabanni daban-daban na siyasa ba don son kai ba ne, sai don kare dimokaradiyya
  • Tsohon Gwamnan ya jaddada cewa duk wani dan Najeriya na da hakki ya yi magana don a kawo gyara a yadda ake mulkarsa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar JigawaSule Lamido, daya daga cikin dattawan jam’iyyar adawa ta PDP, ya ce ba za su gaji wajen kira da ƙoƙarin haɗa duk wani mai faɗa-a-ji a siyasar Najeriya ba.

Ya ce manufarsu ita ce tabbatar da cewa dimokaradiyya ta dore, kuma kasar ta samu ci gaba mai ɗorewa domin kowa ya samu sauki.

Kara karanta wannan

Bugaje: Tsohon dan majalisa ya 'karyata' Obasanjo kan neman wa'adi na 3

Sule Lamido ya ce ana aikin hada kan yan siyasa
Hoton tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido Hoto: Sule Lamdio
Source: Twitter

A hirarsa da BBC, Sule Lamido, wanda tsohon Gwamnan Jigawa ko shakka babu, su na tattaunawa da shugabannin siyasa daban-daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sule Lamido: Ana son haɗa kan yan siyasa

A cewar tsohon Gwamnan, ana tattaunawa ne saboda cwato al'ummar Najeriya baki dayansu, ba wai saboda son rai ba.

Ya ƙara da cewa, PDP na ƙoƙari ainun don ganin ta warware matsalolinta na cikin gida domin ta fito da ƙarfin da ake bukata wajen jan ragamar ƙasa.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya saba haduwa da tsofaffin abokan siyasa irin su Atiku Abubakar, wanda suka taba yin jam’iyya ɗaya a baya.

Sule Lamido ya ce ba laifi a fada wa Tinubu gaskiya
Hoton Sule Lamido, da Shugaba Bola Tinubu Hoto: Sule Lamido/Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce:

"Ko da kuwa mun rabu da jam’iyya ɗaya, dukkanninmu ‘yan Najeriya ne, kuma muna da muradin ganin kasa ta ci gaba. Don haka tattaunawa da kowa ba laifi ba ne.”

Haka zalika, Sule Lamido ya ce ya gaisa da shugaban kasa Bola Tinubu a kwanakin baya saboda tarihi ya haɗa su tun daga jam’iyyar SDP.

Kara karanta wannan

'A ina 'yan bindiga ke samun makami?' An yi wa Tinubu tambaya mai zafi

Sule Lamido: Kowane dan kasa na da hakki

A cewarsa, ko da yake yanzu su ba jam’iyya ɗaya, Tinubu shugaban ƙasa ne, kuma hakkin kowa ne a matsayin ɗan kasa ya yaba ko ya suke shi idan ya yi kuskure.

Ya ce:

“Idan shugaban ya yi daidai, za mu yaba. Idan kuma bai yi daidai ba, mu fada gaskiya domin gyara. Wannan ba suka ba ne, gyara ne."

Tsohon Gwamnan ya jaddada cewa, burinsu shi ne ganin Najeriya ta samu shugabanci nagari da kuma makoma mai kyau.

Sule Lamido ya ba 'yan hadaka shawara

A wani labarin, kun ji cewa Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana ra’ayinsa game da hadakar ‘yan adawa da ke karkashin ADC.

Ya ce duk da ya halarci kaddamar da jam’iyyar ADC a watan Yuli, har yanzu yana nan daram cikin jam’iyyar PDP, kuma bai da niyyar barinta sai dai za a ci gaba da aiki tare.

Kara karanta wannan

2027: Gangar siyasa ta fara kaɗawa, Sanata ya ƙaddamar da kungiyar zaɓen Tinubu

Sule Lamido ya gargadi ‘yan takara da ke karkashin jam’iyyar ADC da su rage gaggawan neman madafun iko da kuma yin taka-tsantsan a shirye-shiryensu na 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng