Kwankwaso Ya Karbi 'Dan Takarar Gwamna zuwa NNPP, Kwankwasiyya na Murna
- Tsohon ɗan takarar gwamna na jihar Kogi a karkashin jam’iyyar YPP, Dr Sam Omale, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP
- Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce gogewar Omale a fannin kuɗi da kasuwanci za ta taimaka wajen ciyar da jam’iyyar gaba
- Kwankwasiyya ta bayyana shigowar Dr Omale a matsayin babban ci gaba ga jam’iyyar da kuma makomar tarayyar Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi Dr Sam Omale, tsohon ɗan takarar gwamnan Kogi a jam’iyyar YPP zuwa NNPP.
Taron ya gudana ne a gidan Kwankwaso da ke Maitama, Abuja, inda aka bayyana wannan mataki a matsayin wani sabon babi ga jam’iyyar NNPP.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka karbe shi zuwa NNPP ne a wani sako da hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauya shekar Dr Omale, wanda yake gogaggen masanin harkokin kuɗi a Najeriya da Birtaniya, ta jawo farin ciki ga 'yan Kwankwasiyya, tare da fatan zai taimaka wajen ƙarfafa NNPP.
'Dan takarar gwamna ya shiga NNPP
Dr Sam Omale, wanda ya yi takarar gwamnan Kogi a jam’iyyar YPP, ya bayyana cewa shawarar shigarsa NNPP da Kwankwasiyya ta samo asali ne daga burinsa na ganin Najeriya ta ci gaba.
Ana sa ran Dr Omale zai kasance daga cikin jagororin jam'iyyar NNPP a jihar Kogi da ma Arewa ta Tsakiya.
Gogewa da ƙwarewar Sam Omale
An bayyana Dr Omale a matsayin kwararren masani a fannin kuɗi, wanda ya shafe sama da shekaru 25 yana aiki a manyan bankuna a Najeriya da Birtaniya.
Saboda kwarewar da yake da ita, Vanguard ta wallafa cewa ya taba zama mamba a kwamitocin gudanarwa na wasu bankuna.
Shi ne wanda ya kafa Rock Global Training & Consultancy, wani kamfani da ke mayar da hankali kan harkokin kasuwanci da dabarun kuɗi.
Omale ya yi karatu a manyan jami’o’i ciki har da Ahmadu Bello da ke Zariya, jami'ar Nsukka da kuma jami'ar Brighton a Birtaniya, inda ya samu kwarewa a harkar kudi.

Source: Facebook
'Yan Kwankwasiyya sun yi murna
Saifullahi Hassan ya bayyana cewa 'yan Kwankwasiyya na maraba da shigowar Dr Omale da hannu biyu-biyu.
A cewarsa, gogewa da zurfin iliminsa za su taimaka wajen gina jam’iyya mai ƙarfi da kuma tsara Najeriya mai ingantacciyar makoma.
Ya ƙara da cewa wannan ci gaba yana nuna yadda NNPP ke jan hankalin manyan ƙwararru da masu kishin ƙasa daga sassa daban-daban domin su haɗa kai wajen tafiyar da manufofi nagari.
NNPP ta barranta da Rabiu Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa tsagin jam'iyyar NNPP ya yi martani kan maganar shiga APC da Rabiu Kwankwaso ya yi.
Tsagin jam'iyyar ya bayyana cewa ya riga ya sallami Kwankwaso da 'yan Kwankwasiyya daga NNPP tun da dadewa.
Baya ga haka, ya ce ya mayar da hankali ne wajen ganin NNPP ta fuskanci zaben 2027 da gaske ba wai shiga APC ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

