Fitaccen Jarumin Fim Ya Hango Jam'iyyar da Za Ta Iya Kifar da Tinubu a Zaben 2027

Fitaccen Jarumin Fim Ya Hango Jam'iyyar da Za Ta Iya Kifar da Tinubu a Zaben 2027

  • 'Dan siyasa kuma jarumi a masana'antar Nollywood, Kenneth Okonkwo ya ce bai kamata zaben cike gurbi ya zama gwajin karfin ADC a Najeriya ba
  • Okonkwo ya bayyana cewa jam'iyyar hadaka ta shirya tsaf domin karbe mulki daga hannun Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Fitaccen jarumin ya kuma bayyana tsohon gwamna, Rotimi Amaechi a matsayin jagoran ADC a jihar Ribas

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Fitaccen jarumin Nollywood kuma ɗan siyasa, Kenneth Okonkwo, ya bayyana cewa jam’iyyar hadakar yan adawa watau ADC za ta lashe zaben 2027.

Jarumin masana'antar shirya fina-finan Najeriya ya bayyana kwarin gwiwa cewa ADC za ta karɓi mulki daga hannun gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Jarumin Nollywood, Okonkwo.
Hoton fitaccen jarumin Nollywood ta Najeriya, Kenneth Okonkwo Hoto: Kenneth Okonkwo
Source: Twitter

Okonkwo ya faɗi haka ne a lokacin da yake jawabi a shirin Sunrise na tashar Channels TV a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

El Rufai ya gargadi 'yan Najeriya kan Tinubu, ya yi hasashen shirinsa kan mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan za ku iya tunawa ADC ta ce bai kamata a auna sakamakon zaben cike gurbin da aka yi kwanan nan, da zaben 2027 ba.

Hukumar zabe (INEC) ta gudanar da zaben cike gurbi na 'yan Majalisar Tarayya da na jihohi a mazabu 16 ranar 16 ga watan Agusta, 2025.

Sai dai sakamakon zaben ya nuna cewa ADC ba ta ci ko da kujera daya ba, yayin da APC mai mulki ta lashe kujeru 12 cikin 16.

Jam'iyyar ADC na da dama a zaben 2027?

Wannan sakamakon ya sa aka fara tunanin da wuya ADC ta kai labari a zaben 2027, lamarin da jam'iyyar ta musanta.

Da aka tambaye shi ko ADC na da damar yin nasara a 2027, Okonkwo ya ce:

“Muna da damar samun nasara a kowane zaɓe a Najeriya.”

Sai dai ya yi ikirarin jama'a sun shiga shakku a kan zabukan fitar da gwanin da ADC ta gudanar kafin sabon shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin David Mark ya hau kan mulki.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Shugaban APC ya rikita 'yan adawa kan zaben 2027

Abin da ya ci ADC ta fadi zaben cike gurbi

"Ba zan ce komai ba saboda an fitar 'yan takara kafin nada sabon shugabancin ADC karkashin Sanata David Mark. Ba mu cikin wadanda suka yanke hukunci a wancan lokacin.
"Bisa haka ina ganin lokacin gwajin ADC shi ne zaben 2027, a lokacin za a gane karfin da jam'iyyar ke da shi. Muna shirin kafa gwamnatin Najeriya ta gaba, mu maida Tinubu zuwa Bourdillon.”

- In ji Okonkwo.

Kenneth Okonkwo.
Hoton jarumin Nollywood, Kenneth Okonkwo da na Bola Tinubu Hoto: Kenneth Okonkwo, @aonanuga1956
Source: Twitter

Jarumi Okonkwo yana goyon bayan Amaechi

Da aka tambaye shi kan tsarin jam’iyyar a Jihar Ribas, Okonkwo ya tabbatar da cewa ADC na da tsarin aiki a dukkan jihohin 36 na Najeriya.

Jarumin Nollywood ya kuma tabbatar da cewa tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi shi ne jagoran jam’iyyar ADC a Ribas, kamar yadda Punch ta rahoto.

ADC ta shirya sauya tsarin siyasar Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta bayyana shirinta na gyara salon siyasa a Najeriya idan ta samu mulki a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Jonathan ya kada hantar shugabanni, ya fadi abij da ya kamata a yi wa marasa katabus

Sakataren jam'iyyar, Rauf Aregbesola ya bayyana cewa ADC ta yi niyyar kawar da tasirin ubangida, amfani da kudi daga tsarin siyasar kasar nan.

Tsohon ministan harkokin cikin gidan ya bayyana cewa akidar ADC ita ce kafa gwamnati mai kula da jama’a, wacce za ta tsamo kasar nan daga mawuyacin hali.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262