Da Gaske Tinubu zai Zauna a Mulki har Ya Mutu? Fadar Shugaban Kasa Ta Magantu
- Fadar shugaban ƙasa ta karyata ikirarin Nasir El-Rufa’i da ya ce Bola Tinubu na shirin zama shugaba har mutuwa
- An bayyana cewa Tinubu ɗan dimokuraɗiyya ne kuma ba shi da niyyar wuce Mayun 2031 a kan karagar mulki
- Fadar ta ce El-Rufa’i ya shiga yada jita-jita ne bayan ganin irin goyon bayan da Tinubu ke samu a Arewacin Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Fadar shugaban ƙasa ta yi magana kan zargin da aka yi wa Bola Tinubu na cewa zai nemi wuce wa'adi na biyu idan ya zarce.
Wannan na zuwa ne bayan ikirarin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, wanda ya zargi shugaban ƙasa da shirin wuce ƙa’idar mulki.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa ya wallafa a X, Bayo Onanuga ya ce kalaman El-Rufa’i ba su da tushe.

Kara karanta wannan
Kafa bataliya da wasu manyan alƙawura 4 da Tinubu ya yi wa Katsina kan ƴan bindiga
A cewar fadar shugaban ƙasa, tsohon gwamnan ya fara nuna damuwa da yadda Tinubu ke ci gaba da samun karbuwa musamman a Arewacin Najeriya.
Onanuga ya ce El-Rufa'i ya rude
Sanarwar ta ce bayan tarbar da Tinubu ya samu a Kaduna kwanan nan, El-Rufa’i ya shiga yada jita-jita na cewa shugaban ƙasa na dindindin.
Fadar shugaban kasa ta bayyana maganar da Nasir El-Rufa'i ya yi a matsayin abin dariya da kuma ƙarya marar tushe.
Mai magana da yawun Tinubu ya ce:
“El-Rufa’i ya rasa hujja, don haka ya koma yada ƙaryar cewa shugaban ƙasa na shirin zama a mulki bayan 2027. Wannan batu ba shi da tushe kuma ba shi da ma’ana.”
Tinubu ba zai wuce wa'adi 2 ba
A cewar sanarwar, shugaban ƙasa Tinubu mutum ne mai bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya kuma ba ya da niyyar karya dokokin mulki.
“Shugaban ƙasa ba zai wuce Mayu 28, 2031 a mulki ba, idan Allah ya nufa ya sake cin zabe a 2027,”
- In ji sanarwar.
Haka kuma Onanuga ya ce gwamnoni da shugabanni a Arewa sun nuna goyon bayansu ga Tinubu a lokacin da El-Rufa’i na ƙoƙarin yada labaran da za su rage masa farin jini.
Tribune ta wallafa cewa sanarwar ta ƙara da cewa:
“Gwamna Uba Sani zai iya taimaka wa magabacinsa, domin ya kamata El-Rufa’i ya samu shawarwari daga masana,
"Saboda yana ta fadan zantukan karya da kuma ƙoƙarin ƙirƙiro tatsuniyoyi kan 2027.”
Onanuga ya bayyana cewa wannan halayyar ta nuna cewa El-Rufa’i da abokan siyasa a sabuwar jam’iyyarsa sun kasa cimma burin hana Tinubu samun nasara a 2027.

Source: Facebook
Tinubu ya je gidan Buhari a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa manyan Najeriya ciki har da gwamnoni ne suka raka shugaba Bola Tinubu jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa shugaban kasar ya ziyarci Kaduna ne domin ganawa da matar marigayi shugaba Muhammadu Buhari da daurin aure.
A cikin jawabin da shugaban kasar ya yi, ya nuna cewa zai cigaba daga tubalin da Muhammadu Buhari ya daura a Najeriya.
Asali: Legit.ng

