Tsohon Shugaban APC Na Kasa, Abdullahi Adamu Ya Fice daga Jam'iyyar? An Samu Bayani
- An yada jita-jitar cewa tsohon shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya fice daga jam'iyya mai mulki a Najeriya
- Shugaban APC na karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa, Alhaji Mohammed Bello Soja, ya fito ya yi martani kan jita-jitar
- Alhaji Mohammed Bello Soja ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Nasarawa bai fice daga jam'iyyar APC ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Nasarawa - Shugaban APC na karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa, Alhaji Mohammed Bello Soja, ya yi magana kan jita-jitar cewa Abdullahi Adamu, ya fice daga jam'iyyar.
Alhaji Mohammed Bello Soja ya karyata jita-jitar da ke cewa tsohon gwamnan Nasarawa Abdullahi Adamu ya fice daga jam’iyyar APC.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta ce Alhaji Mohammed Bello Soja, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ta yi da shi.

Kara karanta wannan
Kasa da shekara 1 bayan shan kashi a zabe, 'dan takarar gwamnan PDP ya shirya komawa APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Abdullahi Adamu dai ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar APC ne a cikin watan Yulin shekarar 2023.
Shin Abdullahi Adamu ya bar APC?
Alhaji Mohammed Bello Soja ya ce kasancewarsa shugaban APC a karamar hukumar da Abdullahi Adamu ya fito, yana iya tabbatar da cewa tsohon shugaban jam'iyyar na kasa bai fice daga jam'iyyar ba.
Ya bayyana cewa har yanzu Abdullahi Adamu ɗan jam’iyya ne mai aiki tukuru, yana shiga tare da halartar dukkan ayyukan jam’iyya daga matakin mazaba har zuwa jiha.
Hakazalika ya bayyana cewa a halin yanzu, Sanata Abdullahi Adamu, ne ke jagorantar aikin neman kujerar gwamna na Nasarawa ta Yamma a karkashin tutar APC.
Wace rawa yake takawa a APC?
Ya kuma kara da cewa yana dagewa wajen ganin jam’iyyar ta ba yankin Nasarawa ta Yamma damar tsayar da ɗan takarar gwamna a zaben shekarar 2027.
Alhaji Mohammed Bello Soja ya bayyana Abdullahi Adamu a matsayin jagoran APC na yankin mazabar sanatan Nasarawa ta Yamma kuma babban jigo a jihar.
Hakazalika ya jaddada cewa tsohon gwamnan na ci gaba da jajircewa wajen ganin jam’iyyar ta yi nasara a dukkan matakai.
Ya roƙi jama’a da su yi watsi da ikirarin cewa Sanata Abdullahi Adamu ya koma jam’iyyar ADC, yana mai kiran zancen a matsayin marar tushe kuma tsabagen yaudara.

Source: UGC
Karanta wasu labaran kan jam'iyyar APC
- Tirkashi: Shugaban APC ya rikita 'yan adawa kan zaben 2027
- Kasa da shekara 1 bayan shan kashi a zabe, 'dan takarar gwamnan PDP ya shirya komawa APC
- 2027: Yadda Kwankwaso ya sha yabo da raddi kan maganar yiwuwar shiga APC
- Shugaban APC ya yabi manufofin Tinubu, ya fadi sauyin da suka kawo a Najeriya
'Yan APC sun ba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar APC North Central Forum, ta yi kira da babbar murya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya daina sakin fuska ga gwamnonin jjam'iyyun adawa masu zuwa wajensa.
Ta bayyana cewa da yawa daga cikin wadannan gwamnonin suna muzgunawa mambobin jam'iyyar APC a jihohinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
