'Yan APC Sun Ankarar da Shugaba Tinubu kan Gwamnonin da Zai Yi Hattara da Su

'Yan APC Sun Ankarar da Shugaba Tinubu kan Gwamnonin da Zai Yi Hattara da Su

  • Wata kungiyar jam'iyyar APC ta ba da shawara ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan gwamnonin jam'iyyun adawa
  • Kungiyar ta bukaci shugaban kasan da ya daina sakar musu fuska don suna tsangwamar 'ya'yan APC a jihohinsu
  • Ta bayyana cewa gwamnonin suna amfani ne da kusancin da su ke da shi ga Shugaba Tinubu wajen gyara siyasarsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ƙungiyar APC North Central Forum ta yi kira da babbar murya ga Shugaba Bola Tinubu.

Kungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu da ya ja kunnen gwamnonin jam’iyyun adawa da ake zargin suna tsanantawa da muzgunawa ga mambobin APC a jihohinsu.

'Yan APC sun ba Tinubu shawara
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Jaridar The Nation ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Saleh Zazzaga, ya fitar a ranar Lahadi, 21 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

El Rufai ya gargadi 'yan Najeriya kan Tinubu, ya yi hasashen shirinsa kan mulki

Wace shawara aka ba Shugaba Tinubu?

Ya shawarci Shugaba Tinubu da masu ba shi shawara da su daina sakin fuska ga gwamnonin adawa, yana zarginsu da yin shirin yaudara da nuna biyayya a zahiri amma suna lalata APC a jihohinsu.

Ƙungiyar ta yi gargadin cewa ci gaba da kyakkyawar alaƙar shugaban kasa da irin waɗannan gwamnonin na iya rage karfin gwiwar mambobin jam’iyyar tare da raunana karfin APC kafin zaɓuɓɓuka masu zuwa.

"Muna rokon Shugaba Bola Tinubu da ya daina sakin fuska ga gwamnonin jam’iyyun adawa da suke zuwa wajensa da yaudara da karya."
"Suna fadin kalmomi masu daɗi idan sun gana da shugaban kasa, amma da zarar sun koma jihohinsu suna yin abubuwa daban.”

- Saleh Zazzaga

An ankarar da Tinubu kan halin wasu gwamnoni

Kungiyar ta ƙara da cewa irin waɗannan gwamnonin suna amfani da kusancinsu da shugaban kasa wajen gyara siyasarsu, yayin da kuma suke ci gaba da tauye hakkin mambobin APC a jihohinsu, rahoton Vanguard ya tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Shugaban APC ya rikita 'yan adawa kan zaben 2027

“Suna nuna halin kirki idan suna gaban shugaban kasa, amma da zarar sun koma jihohinsu suna ɗaukar matakai da suka sabawa muradun shugaban kasa da APC."
"Waɗannan gwamnonin suna tsoratar da mambobin APC marasa laifi a jihohinsu. Har suna kai ga amfani da karfin gwamnati wajen tozarta harkokin kasuwancin mambobin APC masu bin doka waɗanda suke kokarin neman abin dogaro.”

- Saleh Zazzaga

'Yan APC sun ba Shugaba Tinubu shawara
Shugaban kasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

A cewar sanarwar, kungiyar ta ce mambobin APC a jihohin da jam’iyyar adawa ke mulki sun sha fuskantar tsangwama, har da kai ga yi wa kasuwancinsu barazana ko kuma a yi wa kadarorinsu alamar rushewa.

"Ci gaba da karɓar waɗannan gwamnonin adawa zai sa a yi tunanin cewa kamar Shugaba Bola Tinubu na goyon bayan danniyar da ake yi wa mambobin APC a jihohinsu."

- Saleh Zazzaga

El-Rufai ya soki gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ragargaji gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

El-Rufai ya yi zargin cewa gwamnatin Tinubu ta kama hanyar zama ta kama-karya duba da yadda take babbake komai.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya samu gagarumin tagomashi yayin da ake tunkarar zaben 2027

Tsohon gwamnan ya yi gargadin cewa idan har 'yan Najeriya ba su kawar da Tinubu ba a zaben 2027, yana iya zama kamar shugaban kasan Kamaru, Paul Biya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng