Tirkashi: Shugaban APC Ya Rikita 'Yan Adawa kan Zaben 2027

Tirkashi: Shugaban APC Ya Rikita 'Yan Adawa kan Zaben 2027

  • Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yiltwatda, ya tabo batun babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta shirya tsaf don tunkarar zaben
  • Shugaban na APC ya kuma nuna cewa a shirye jam'iyyar take wajen ganin ta lashe dukkanin kujerun da za ta fafata zabe a cikinsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa jam’iyyar ta shirya tsaf domin zaɓen 2027.

Farfesa Nentawe Yilwatda ya jaddada cewa babu wata hadaka da za ta hana APC lashe kujerun shugaban kasa, gwamnoni da sauran kujeru a faɗin kasar nan.

Shugaban APC ya ce jam'iyyar ta shirya zaben 2027
Hoton shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce ya faɗi haka ne a yayin wani shiri a tashar Jay FM 101.3 da aka gudanar a Jos, babban birnin jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Jonathan ya kada hantar shugabanni, ya fadi abij da ya kamata a yi wa marasa katabus

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan adawa na son kifar da Tinubu

Shugabannin adawa suna ci gaba da tsara dabaru domin hana Shugaba Tinubu sake lashe zaɓen 2027, suna zargin cewa mulkinsa ya jefa kasar nan cikin yunwa, talauci, rashin aikin yi, da rashin tsaro.

Sai dai fadar shugaban kasa da jam’iyyar APC sun sha musanta waɗannan zarge-zarge, suna masu cewa karya ce mara tushe, tare da bayyana gwamnatin a matsayin wadda ke bakin kokarinta.

Me shugaban APC ya ce kan 2027?

Farfesa Yilwatda ya ce babu wani taron dangi da zai iya kayar da APC, inda ya bayyana dukkan jam’iyyun adawa ciki har da ADC a matsayin waɗanda tasirin su ya takaita ne kawai a wasu kananan wurare.

Ya kawo misali da nasarar da APC ta samu a zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihohi 12 a baya-bayan nan, yana mai cewa irin wannan sakamako zai sake fuskantar jam’iyyun adawa a 2027.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya samu gagarumin tagomashi yayin da ake tunkarar zaben 2027

Nentawe Yilwatda ya karyata zargin cewa APC na kokarin jefa Najeriya karkashin jam’iyya ɗaya, ko kuma tana da hannu a rikice-rikicen cikin gida da suka addabi manyan jam’iyyun adawa.

Nentawe ya soki 'yan hadaka

Ya kuma bayyana haɗin gwiwar jam’iyyun adawa a matsayin “auren dole” wanda daga bisani zai tarwatse.

Shugaban APC ya ragargaji 'yan hadaka
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Shugaban na APC ya bayyana cewa sababbin manufofin Shugaba Tinubu sun ba jihohi damar samun karin kuɗaɗe da biyan albashi cikin sauki ba tare da ciyo bashi ba.

Ya ce manufofin Shugaba Tinubu sun ba jihohi damar tara manyan kudaden shiga, gudanar da ayyukan raya kasa yadda ya kamata, lamarin da ya sa wasu gwamnonin adawa ke sauya sheka zuwa APC.

Jigo a PDP ya shirya komawa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar gwamnan jihar Ondo a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Hon. Agboola Ajayi, ya shirya komawa APC.

Agboola Ajayi ya shirya komawa APC ne bayan ya janye karar da ya shigar a gaban Kotun Koli, inda yake kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar na watan Nuwamban 2024.

Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya bayyana cewa Agboola Ajayi ya sanar masa da cewa zai sauya sheka zuwa APC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng