Siyasa: Atiku Ya Ziyarci Pantami, Sun Tattauna Batun Shugabanci da Sauransu

Siyasa: Atiku Ya Ziyarci Pantami, Sun Tattauna Batun Shugabanci da Sauransu

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Pantami, a gidansa
  • Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa masu muhimmanci kamar tattalin arziki, ilimi, da sauransu
  • Atiku ya kuma karɓi Nafisa Abdullahi, wacce ta lashe gasar TeenEagle a Birtaniya, tare da ba ta tallafin karatu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

ABUJA – Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa ya karɓi tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, a gidansa da ke Abuja.

Ziyarar ta gudana ne a daren jiya inda aka tattauna kan batutuwa masu muhimmanci da suka shafi ci gaban kasa.

Atiku yana tattaunawa da Sheikh Pantami a Abuja
Atiku yana tattaunawa da Sheikh Pantami a Abuja. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano abubuwan da suka tattauna ne a wani sako da Sheikh Isa Ali Pantami ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Wike ya fadi abin da ƴan siyasar Ribas suka saka a gaba bayan dawowar Fubara

Pantami ya ce Atiku ya kawo masa wannan ziyara ta zumunci, kuma suka yi hira ta musamman kan fannoni da suka shafi tattalin arziki da sauransu.

Me Pantami ya tattauna da Atiku?

Pantami ya bayyana cewa ziyarar Atiku ba ta zumunci bace zalla, baya ga haka ya ce wata dama ce da suka samu ta tattauna muhimman batutuwa da ke da tasiri ga makomar Najeriya.

Ya ce batutuwan da aka tabo sun hada da hanyoyin farfado da tattalin arziki, a ilimi, da kuma tabbatar da shugabanci nagari.

Sheikh Pantami ya bayyana cewa shi da iyalansa suna mika godiya ga Atiku Abubakar bisa wannan ziyarar da ya kai musu.

An dade ana kira ga Sheikh Isa Ali Pantami da ya fito takarar gwamna a jihar Gombe, amma yana bayyana cewa sai lokaci ya yi zai fitar da matsayarsa kan kiran.

Atiku ya gana da Nafisa Abdullahi

Kara karanta wannan

Mambilla: EFCC ta maida tsohon minista gaban kotu kan zargin almundahanar $6bn

A wani labarin kuma, Atiku Abubakar ya karɓi Nafisa Abdullahi, ‘yar Najeriya da ta lashe gasar TeenEagle a Birtaniya, a gidansa da ke Abuja.

Atiku ya bayyana farin cikinsa da ganin nasara irin wannan daga matasan Najeriya, yana mai cewa lallai wannan gagarumar nasara ce da ke nuna irin hazaka da basirar matasan kasar.

Ya bayyana cewa ya yi amfani da damar wajen tabbatar da alkawarin da ya dauka na tallafawa Nafisa da abokan karatunta biyu da suka yi nasara tare da ita ta hanyar bayar da tallafin karatu.

Atiku tare da Nafisa da ta lashe gasar Turanci
Atiku tare da Nafisa da ta lashe gasar Turanci a London. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Kalaman Atiku kan matasan Najeriya

A sakon da ya wallafa a X, Atiku ya ce yana da cikakken imani da kaifin basirar matasan Najeriya, kuma hakan ne yasa ya dage wajen ganin an maida hankali a kan ilimin matasa.

Ya jaddada cewa makomar Najeriya za ta dogara ne da yadda ake bai wa matasa damar yin amfani da ilimi da fasaharsu.

Atiku ya karbi 'yan CPC a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gana da tsofaffin shugabannin tsohuwar jam'iyyar CPC.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Abba Kabir ya kalubalanci mulkin Ganduje, ya yi masa gorin ayyuka

Tsofaffin shugabannin jihohi na jam'iyyar sun bayyana cewa sun koma bayan Atiku Abubakar da ADC domin ceto Najeriya.

Sun kara da cewa gwamnatin Bola Tinubu ta kaucewa manufar kafa jam'iyyar APC da Muhammadu Buhari ya amince da ita.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng