Ribas: Peter Obi Ya Zargi Gwamnatin Najeriya da Yi Wa Dimokuradiyya Kisan Mummuke

Ribas: Peter Obi Ya Zargi Gwamnatin Najeriya da Yi Wa Dimokuradiyya Kisan Mummuke

  • Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya sake dura a kan gwamnatin Najeriya, a wannan lokacin, yana zarginta da kashe dimokuradiyya
  • Ya bayyana cewa siyasa a Najeriya ta rikide zuwa hanyar amfani da dukiyar ƙasa domin son rai da biyan bukatun iyalai
  • Obi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su zabi shugabanni nagari domin dawo da dimokuraɗiyyar da za ta amfane su

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers – Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya bayyana cewa dimokuraɗiyya na mutuwa sannu a hankali a Najeriya.

Tsohon dan takarar ya fadi haka ne saboda a cewarsa, yanzu dimokuradiyya ta daina amfanar jama’a, kuma ba ta iya kama shugabanni bisa abin da su ke aikata wa.

Kara karanta wannan

Bayan barazanar Isra'ila, Saudi ta kulla yarjejeniyar tsaro da Pakistan mai nukiliya

Peter Obi ya soki dimokuradiyya a Najeriya
Hoton tsohon dan takarar Shugaban Kasa, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba, ta cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X bayan ya halarci wani taron shekara-shekara da gidauniya Goodluck Jonathan ta shirya a birnin Accra, Ghana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi ya caccaki gwamnatin Najeriya

A sakon, Obi ya ce Najeriya misali ce ta inda dimokuraɗiyya ke mutuwa, saboda rashin adalci da rashin tallafa wa talakawa.

'Dan siyasar ya nuna cewa tsarin mulkin kasar ya rikice, inda wasu kalilan ke cin gajiyar arzikin ƙasa yayin da yawancin al’umma ke cikin kunci.

Obi ya ce wasu 'yan tsiraru ke morar Najeriya
Hoton daya daga cikin jiga-jigan 'yan adawa, Obi Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

A cewarsa:

“Dimokuraɗiyya na mutuwa ne idan jama’a ba su san halin da ake ciki ba, kuma idan ba ta dora bukatunsu a gaba ba.”
“Najeriya ita ce misalin inda dimokuraɗiyya ke mutuwa domin ba ta amfana wa jama’a komai."

Obi: 'Yan tsiraru ke amfana da gwamnati

Obi ya ce dimokuraɗiyyar Najeriya yanzu ta rikide zuwa tsarin da ke bai wa wasu shafaffu da mai damar amfani da albarkatun ƙasa don amfanin kansu da na danginsu.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi nazari, ya gano abin da yake tunanin ya hana kawar da 'yan bindiga a Najeriya

Ya ce:

“A Najeriya, dimokuraɗiyya ta koma hanyar cin moriyar dukiyar al’umma don bukatun kan wasu da iyalansu.”

Obi ya ce hanya ɗaya tilo da za a iya ceto dimokuraɗiyya ita ce idan ‘yan kasa suka farka, suka zabi shugabanni masu gaskiya, kwarewa, tausayi, da jajircewa wajen aiki yadda ya dace.

Ya kuma bayyana dokar ta baci a Jihar Ribas a baya a matsayin babban kuskure da ke ci gaba da kawo cikas ga dimokuraɗiyya.

A kalaman tsohon gwamnan:

“Mayar da dimokuraɗiyya a Jihar Ribas bayan watanni shida bai da wani amfani, har yanzu tangarda ce ga dimokuraɗiyyar Najeriya.”

Obi ya ce hakan ya sabawa kundin tsarin mulki kuma yana barazana ga dorewar siyasar gaskiya da adalci ga masu kada kuri'a.

LP ta kalubanci Peter Obi

A baya, kun ji cewa Jam’iyyar LP ta raba gari da tsohon dan takararta, inda ta bayyana cewa ba ta da niyyar ba Peter Obi tikitin takarar shugaban kasa a zaɓen shekarar 2027 mau zuwa.

Kara karanta wannan

'Yan fansho sun fusata, suna shirin fara zanga zanga tsirara a fadin Najeriya

Wannan jawabi ya fito ne daga Sakataren yada labaran kasa na jam’iyyar, Abayomi Arabambi, a ranar Litinin, 8 ga watan Satumba, 2025 yayin da jam'iyyu ke shirin zaben 2027.

Ya bayyana cewa salon siyasar Peter Obi ya sha bambam da na LP, saboda haka za su ci gaba da shirin tunkarar babbann zabe mai zuwa ba tare da neman shi ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng